Yan Boko Haram 45ne a kurkukun Kirikiri
– Wata kungiya mai rajin kare hakkin Fursuna, (PRAI), ta nemi a gudanar da bincike akan wasu wadanda ake zargin yan Boko Haram ne a gidan yari na Kirikiri
– PRAI ta rubuta wasika zuwa ga Amnesty International domin kare hakkin wadanda ake zargin
– Wadanda ake zargin, jami’an hukumar DSS ne suka kanan su a shekarar data wuce
Yan kungiyar Boko haram
Sama da yan kungiyar Boko Haram uda 45 ne aka kulle a gidan yari na kirikiri dake a Jihar Legas.
Jaridar The Nation ta bayyana ta bayyana cewa an kulle sune kimanin watanni 7 da suka wuce bayan umurnin da mai shari’a Adeola Adedayo na kotun Isolo dake legas.
Kungiyar ta nemi kungiyar Amnesty international data gudanar da bincike domin ta gano gaskiyar lamarin domin a fidda masu hakkin su.
Idan zaku iya tunawa, a shekarar data wuce, jami’an hukumar DSS sun kama yan Boko Haram guda 45 bayan da suka lalata shirin su na tada bam a Dolphin estate, Ikoyi, Jihar Legas.
Wadanda ake zargin an kaisu kotun Isolo inda Alkali mai Shari’a ya bada murni a kulle su a gidan yari na kirikiri dake a cikin garin Legas.
Kiran nasu an sanya mashi hannu ne a ranar 5 ga watan Afrillu inda Ahmed Adeola kazeem ya sanya ma takardar hannu.
Kiran kuma an aika shi ga shugaban masu gurfanarwa na Najeriya, kuma Ministan shari’a da kuma kwamishinan Shari’a na jihar legas.
Bincike ya nuna cewa sama da mutane 25,000 ne suka rasa rayukan su sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram na shekaru 6, inda kuma sama da mutane Miliyan 3 aka kore su daga gidajen su.
A wani labarin kuma, kasar ingila ta sha alwashin taimaka ma najeriya da Pan Miliyan 43 domin taimaka ma mutanen Arewa maso gabas wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.
The post Yan Boko Haram 45ne a kurkukun Kirikiri appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.