Sojojin Najeriya sunyi artabu da Yan Boko Haram a Wunbi
– Sojojin Najeriya sunyi nasarar dakushe wani hari yan Boko Haram suka so kaima Wunbi
– Rundunar soji ta Birigade na 22 sunyi nasarar maida martabi bayan kare harin
– Wannan yazo ne bayan da suka samu rahotanni
Kanar Kakasheka Usman, jami’i mai hudda da jama’a na sojin Kasa, ya bayyana cewa sojojin Disbishan ta 7 runduna ta 22 sunyi nasarar dakushe wani hari wanda yan Boko Haram suk so kaima karamar hukumar Wunbi Kala balge dake cikin Jihar Borno.
Kanar Usman ya bayyana cewa yan ta’addan sunyi niyyar kai harin ne a ranar Asabar 30 hga watan Afrillu inda sai aka gano su.
Ya bayyana cewa an samu nasarar dakushe harin ne bayan da aka samu rahotannin akan abunda yan kungiyar suke da niyyar aikatawa a karamar hukumar. Sun hadu ne a Takura wadda take kimanin kilomita 20 daga Maiduguri, bayan anyi musaar wuta, daga karshe sojojin Najeriya sunyi nasarar kashe yan ta’adda 9
Jami’in ya bayyana cewa an samu amshe Bindiga kirar AK-47 daga hannun yan ta’adaddan, sannan ya bayyana cewa an amshe RPG, tulin harsashi, Bam na hannun.
Sannan ya bayyana cewa kimanin sojojin Najeriya guda 6 sun samu raunuka inda tuni an kwashe su an kai su asibiti domin duba lafiyar su.
Kanar Kakasheka ya nemi mutanen gari da a kodayaushe su ringa kawo ma sojojin Najeriya bayanai wadanda zasu dakushe kaifin yan ta’addan.
Sojojin najeriya na cigaba da matsa lamba ga yan Boko Haram inda suke samun nasarori akan su a kullu yaumin.
Haka zalika sojojin Najeriya tare da yan kungiyar sa kai sun samu nasarar kakkabe wasu yan Boko haram a Doksa da kuma a sabon garin Doksa.
A wani labarin kuma, sojojin Najeriya sunyi sunyi fata fata da yan Boko Haram a garin Abuja dake a cikin Jihar Borno.
A jiya ne Ministan Tsaron Najeriya, Janar Amnsur Dan ali ya bayyana cewa sojojin Najeriya da sannu zasu gama da yan Boko Haram.
The post Sojojin Najeriya sunyi artabu da Yan Boko Haram a Wunbi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.