Wani soja ya mutu bayan daya taka Nakiyar Yan Boko Haram
– Daya daga cikin sojin da suka taka wata Nakiya wadda yan Boko Haram suka dana ya mutu
– An kashe yan Boko Haram 4 sanadiyyar hakan
– An ceto mutane 400
Daya daga cikin sojojin da suka taka Nakiyar da yan Boko haram ska dana ya rasu. Wannan ya fito ne daga bakin Kanar Kakasheka Usman, Mukaddashin Jami’i mai hudda da jama’a na sojin kasa ya bayyana cewa cikin sojojin guda 4 wadanda suka taka Nakiyar, 1 ne kawai ya mutu amma sauran 3 sun samu raunuka ne kawai.
KU KARANTA: Tsagreun Nija Delta sun ba kabilar Fulani Makonni 2 su bar yankin
A wata wasika ta eail wadda ya aiko ma Naij.com, Kanar Kakasheka Usman, ya bayyana cewa ” Kamar yadda kuka sani, sojojin mu suna aiki awanni 24 a aikin LAFIYA DOLE, domin tabbatar da cewa sun kakkabe ragowar yan ta’addan Boko haram da suka rage.
” Haka zalika, sojojin mu suna aiki daga zuwa yaki, kai farmaki da kuma tare mutane a duba da kuma zagayen dare dana rana.
” Zaku iya tunawa cewa wani soja ya samu rauni sakamakon taka nakiya da yayi da kafar sa. Muna takaicin sanar daku cewa ya rasu, Allah ya jikan shi, ameen.
” Sojojin Runduna ta Birigade ta 22 a fitar ta kwato kauyuka 3 wadanda yan Boko Haram suka amshe, ta kashe yan kungiyar guda 3 a lokacin yaki, sannan kuma sauran da suka ruga suka shige rami an tone ramin kuma an kama su duka.
“Haka zalika sojojin Bataliya ta 3 sun fita aiki akan hanyar su daga Gomboru zuwa Ngala inda suka taka nakiyoyi wadanda yan Bko Haram suka Nada.
” Abun takaici, mun rasa soja 1 da kuma wasu yan kungiyar sa kai. Amma da gawar sojan data yan kungiyar sa kan duka an kauda su daga wurin.
Kanar Kakasheka Usman ya bayyana cewa al’ummar yankin sunfi natsuwa da kokarin da sojojin suke yi wajen tsare rayukan su da kuma dukiyoyin su.
A wani labarin kuma, Shugaban Hafsin Sojin Najeriya, Janar Olanisakin, da Hafsin sojin Kasa, Tukur Buratai, da hafsin sojin Sama sun ziyarci sojojin a bama da Banki inda sukayi masu jinjina kuma suka yaba ma kokarin su.
The post Wani soja ya mutu bayan daya taka Nakiyar Yan Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.