Tsagerun Nija Delta sun ba Fulani Mako 2 su bar yankin
– Tsagerun Nija Delta sun ba Kabilar Fulani wa’adin Mako 2 da su fita daga Yankin ko kuma su fuskanci yaki
– Kungiyar ta baiwa gwamnatin Tarayya wa’adin mako 2 data gano ko suwa nene
– Tsagerun sun bayyana cewa baza su bar Fulani su tafi ba tare da sun dauki fansa ba
Wani makiyayi da Bindiga
Gamayyar kungiyar shugabannnin yan ta’adda na Nija Delta (CML), ta sha alwashin daukar fansa akan kabilar Fulani saboda harin da aka kai a Enugu, idan dai har kabilar Fulani basu bar yankin ba nan da makonni 2 ba.
KU KARANTA: Manyan labarai wadanda sukayi fice a ranar Talata
Jaridar The Sun ta ruwaito wannan labarain daga Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers bayan hare hare wadanda wadansu wadanda ake zargin cewa yan KabilarFulani makiyaya ne suka kai a Uzo-Uwanni dake a Jihar Enugu.
Jami’i mai hudda da jama’a na kungiyar wanda aka fi sani da Janar B, ya bayyana cewa idan dai har wa’adin mako 2 da kungiyar ta ba gwamnatin Tarayya ya cika ba tare da gwamnatin Tarayya ta bayyana ko suwa suka kai harin ba, to zasu fara daukar fansa irin wadda ba’a taba gani ba a Najeriya.
Janar Be ya bayyana cewa kungiyar tasu tayi hakurin jira har gwamnatin ta maganta akan lamarin.
Jami’i mai hudda da jama’a na kungiyar ya bayyana cewa abun takaici ne gwamnatin Tarayya bata nuna wata damuwa sosai ba akan lamarin.
Yace ” Nan da mako 2 daga yanzu idan dai har gwamnatin najeriya bata gaya mana ko wu wanene ba, mu zamu shiga neman ko shu wanene.
janar Ben kuma ya sake jaddada cewa lallai ba zasu bar wannan lamari ya tafi haka nan ba ba tare da sun dauki fansa ba.
Idan za’a iya tunwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen hatre hare da makiyaya suke kaiwa a fadin Tarayyar najerya. Shugaban kasan kuma ya ba sojoji da sauran jami’an tsaro numurni da su kawo karshen lamarin.
The post Tsagerun Nija Delta sun ba Fulani Mako 2 su bar yankin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.