Manyan labarai wadanda sukayi fice a ranar Talata
Naij.com ta tattara maku manyan labarai wadanda sukayi fice a ranar Talata 3 ga watan Mayu na 2016. Ku duba domin ku samu wadannan manyan labaran.
Muhammadu Buhari
1. An fitar da lambobin waya na Gwamnonin Najeriya
An fitar da lambonin waya na gwamnonin Najeriya. Jaridar Sahara Reporters ta fitar dasu.
KU KARANTA: Dole jihohi su biyasabon tsarin kudin ma’aikata – NLC, TUC
2. Anyi halbe halbe a majalisar Jihar Edo
A jiya anyi halbe halbe a majalisar Jihar Edo, inda yan majalisar Jihar suka tsige Kakakin Majalisar Jihar, Mr Victor Edoror
3. Anyi zanga zanga akan harin da Fulani suka kaima Enugu
Wasu mutane a jihar Enugu sunyi zanga zanga akan hare haren da Makiyaya Fulani suka kaima ma wani sashe na Jihar Sunyi zanga zanga ne daga Tashar Holy Ghost zuwa majalisar jihar, zuwa gidan gwamnan Jihar.
4. An kama wadanda manyan Yan Boko haram da suka kashe Janar Mamman Shuwa
An kama wasu Mutane 2 akan zargin kashe Janar Mamman Shuwa. Wadanda aka kama din manyan yan Boko Haram ne.
5. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake maida kasafin Kudin shekarar 2016 Majalisa
Domin ayi wasu gyare gyare a kasafin kudin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake maida kasafin kudin.
6. Kungiyar Atletico Madrid ta fito zuwa wasan Karshe na Champions League
Kungiyar Kwallon Kafa ta Atletico Madrid tayi nasarar fitowa zuwa wasan karshe na Champions League.
7. Daga ina nasarar Leicester City take?
An kafa kungiyar kwallon kafan ne a 1884, ta fara wannan shekarar a matsayin yar baya amma a yanzu itace a sama.
8. Abubuwa masu karya sha’awa
Da yawa mutane suna ciye ciyen abubuwan abinci wadanda basu san ko minene a cikin su ba.
The post Manyan labarai wadanda sukayi fice a ranar Talata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.