Hukumar EFCC ta gayyace Femi Fani Kayode
– Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon jami’i mai hudda da jama’a na kungiyar yakin nean zabe na tsohon shugaban kasa Jonathan
– A jiya ne aka aika mashi da sakon wanda shine na farko wanda hukumar ta taba aika mashi
– A ranar Litinin 9 ga watan Mayu ake tsammanin Femi Fani Kayode ya gurfana a gaban hukumar
Femi Fani Kayode
Akwai alamu cewa hukumar EFCC ta saurari shawarar da Femi Fani kayode ya bata na game da ta gayyace shi hukumar domin yazo yayi masu bayani akan yadda aka rabar da kudaden da PDP ta tara tayi Kampe dasu a yakin neman zabe na 2015.
A wata takarda da hukumar ta aika ma Femi Fani Kayode a ranar Juma’a 6 ga watan Mayu, hukumar ta nei Fani Kayode daya zo ofishin hukumar a ranar Litinin 9 ga watan Mayu.
KU KARANTA: An kama wani matashi saboda rubutu a Facebook
Femi Fani Kayode ya amshi takardar kamar yadda labarin ya zo ma jaridar Naij.com.
Jami’i mai taimaka ma Femi Fani Kayode akan hudda da jama’a, Jude Ndukwe, ya bayyana cewa an aiko da takardar ne a ranar 6 ga watan Mayu, kuma Muhammad Umar ne ya sanya ma takardar hannu a madadin shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu.
Yace ” Hukumar EFCC ta aiko ma mai gida na takarda a yau 6 ga watan mayu na 2016, inda suka nemi daya zo Ofishin hukumar a safiyar Litinin, 9 ga watan Mayu na 2016 domin su tattauna akan wasu lamurra.
” ~Wanna itace takarda ta farko kuma ita kadai ce takardar da hukumar ta taba aiko ma Femi Fani Kayode, wannan ya kara tabbatar da cewa Jaridar The Nation karyata takeyi inda ta buga cewa an aiko ma Femi Fani Kayode takadar gayyata daga EFCC inda ya gudu ya fara boye ma hukumar.
” An kawo takardar gidan shi dake Abuja inda ta hannun Lauyan shi ya tabbatar masu da cewa zaya gurfana a gaban hukumar a safiyar ranar Litinin din.
Haka zalika Jami’i mai hudda da jama’a akan sabbin hanyoyin hudda da jama’a, Deji Adeyanju, ya bayyana cewa yaje gidan Femi Fani Kayode kuma ya ga jami’an hukumar EFCC a wurin. Ya zage su inda ya bayyana cewa sunyi kama da karnuka.
The post Hukumar EFCC ta gayyace Femi Fani Kayode appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).