Ba guduwa nayi domin in boye ba – Jonathan
– Rahotanni na nuna cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ya gudu ya ruga daga Najeriya
– Yawan fice ficen da yake yi daga Najeriya ya sanya ake tsammanin ko guduwa za yayi
– Jonathan ya bayyana cewa baya da wani dalilin da zaya sanya ya gudu ya bara Najeriya
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan
” Ban gudu na ruga ban nazo nan ne don in hutu. Tsohon shugaban kasa Jonathan ya maida martani ga jaridar This Day.
KU KARANTA: Zan hukunta duk dan PDP daya tada rikici – Sefeton Yan sanda
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya maida martani ga Jaridar This Day inda yake magantawa da jaridar a waya bayan da suka buga wani labari cewa ya gudu ya boye a kasar Cote d’ Viore. Tsohon shugaban kasan ya bayyana cewa yazo kasar ne kawai don ya hutu. Ya tabbatar da cewa yaje wasu garuruwa a kasar Amurka, inda daga nan ne ya tafi Ingila sannan ya iso kasar ta Cote d’I Voire ta hanyar Paris.
Ya bayyana cewa baya da wani dalilin da zaya sanya ya gudu ya bar Najeriya domin kuwa yayi ma Najeriya aikin a lokacin da yake shugaban kasa iyakar karfin shi.
” Ana yabo na a duk fadin Nahiyar Afirika aca cewa na hana tashin hankali ta hanyar mika mulki a cikin lumana. Amma da alama cewa Najeriya bata gode mani abunda nayi mata ba.
Jaridar This day ta buga rahotanne inda ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya gudu ya tafi kasar Cot d’ Ivoire domin hukumar hana almundahana tana neman yazo ya amsa tambayoyi.
A watan daya wuce ne shugaban kasar yaje kasar Amurka inda ya amshe lambar girma kuma ya hadu da Andrew Forrest, wani babban attajiri na kasar Australia wanda shine shugaban kungiyar Walk Free Foundation domin tattaunawa akan yadda za’a kawo karshen bauta a Afirika.
The post Ba guduwa nayi domin in boye ba – Jonathan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).