Zan hukunta duk dan PDP daya tada rikici – Sifeton Yan sanda
– Shugaban Yan Sanda, Solomon Arase ya bayyana cewa wasu nasu sutada rikici a cikin Abuja
– Ya bayyana cewa rahoto na nuna wasu shugabanin PDp dake rigima akan kujerar shugaban jam’iyyar ne
– Ya bayyana cewa zasu hukunta duk wanda ya tada rikici
Wasu jami’an yan sanda
Sifeto Janar na Yan sanda, Mista Solomon Arase, ya bayyana cewa sun samu rahoto daga sashen tattara bayanai na hukumar Yan sanda cewa wasu shugabanin jam’iyyar PDP a cigaba da rikicin da sukeyi akan shugabancin jam’iyyar, suna kokarin shigowa Abuja da yan ta’adda domin su amshe Ofishin jam’iyyar.
KU KARANTA: Najeriya ce kasa ta 4 wajen karfin Soja – Rahoto
Sifeton Yan sandan ya bada gargadi ga duk masu kokarin yin hakan inda ya bayyana cewa duk wanda ya tada rikici toh hukumar yan sanda zata hukunta shi da karfin doka.
Yace “Wannan na zuwa ne bayan da rikicin jam’iyyar ya karu inda suka samu rajin jituwa. Kokarin da sukeyi shine su shigo Abuja su amshe Ofishin PDP na kasa domin su shige shi dole.
“Niyyar su shine su shigo suyi zanga-zanga akan tituna, daga nan sai su tafi Ofishin jam’iyyar inda zasu amshe shi da karfin tsiya. Jami’i mai hudda da jama’a na rundunar yan sanda, Olbisi Kolawale ya bayyana hakan.
Ya kuma bayyana cewa shugaban yan sandan ya bada umurni cewa a kara yawan Yan sanda dake a Ofishin Jam’iyyar domin su tsare wurin. Sannan kuma a fiddo da yan sanda na musamman domin tsare tashin hankali, har sai abun ya lafa.
” Wannan mataki da yansa suka dauka anyi hakan ne don kare rikici da kuma karya doka da Oda kamar yadda dokar yan sanda ta bada dama.
Sifeton Yan sandan kuma ya gargadi duka yan siyasa da magoya bayan su da kada suyi wani abu wanda zaya kawo rikici ko kuma karya doka da oda a cikin Najeriya.
Idan za’a iya tunawa, jam’iyyar PDP a ranar 18 ga watan Mayu na 2016, sun gudanar da taro guda 3 daban-daban a Fatakwal, da kuma guda 2 a Abuja inda kowanne suka zabi sabon shugaban jam’iyyar. Wannan ya sanya a yanzu jam’iyyar take da shugabanin jam’iyya guda 3, Ali Modu Sheriff, Ibrahim Mantu, da kuma Ahmad Makarfi
The post Zan hukunta duk dan PDP daya tada rikici – Sifeton Yan sanda appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).