Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin
Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin 23 ga watan Mayu na 2016. Ku duba domin ku samu manyan labaran.
1. Sojojin sun kama ntsagerun Nija Delta masu fasa bututun Mai
Sojojin Najeriya sun kama wasu daga cikin tsagerun Nija Delta wadanda suka fasa bututun Mai na AGIP bayan da suka tada fadan kabilanci.
2. Wani Dan Boko Haram ya halbe mai hada ma kungiyar Bam da wasu manyan kungiyar
Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa, wani dan Boko Haram ya kashe babban mai hada ma kungiyar Bam da wasu manyan kwamandojin kungiyar.
3. Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamnan Ogun
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Gwamnan Ogun Ibikunle Amosun a jiya a fadar shugaban kasa bayan daya fasa tafiyar sa ta kwanaki 2 zuwa Legas
4. Wani Matashi dan shekara20 yayi kokarin halaka kanshi a kasar Chile
Wani matashi dan shekara 20 yayi kokarin hallaka kanshi ta han hanyar shiga kejin zaki zindir. Amma Zakin baiyi nasarar kash shi ba inda aka kashe Zakunan aka cece shi.
5. Tsagerun MEND sun zagi Jonathan
Kungiyar MEND ta fitar da wata takarda inda take sukar Gwamnatin Goodluck Jonathan da sanya Najeriya da Yan Najeriya a cikin tsaka mai wuya.
6. Shugaba Buhari na shirin nada mutumin Jonathan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin nada Timi Alaibi a matsayin shugaban hukumar NDDC. Alaibi ya taba rike mukamin kuma ya taba zama mai ba shugaban kasa shawara akan Afuwar da akayi ma tsagerun yanki.
7. Jonathan na ruga daga Najeriya; Reno Omokri ya maganta
Reno Omokri ya maganta akan cewa cewa shugaban kasa Jonathan ya ruga daga Najeriya bayan daya samu labarai cewa hukumar EFCC na shirin kama shi.
8. Za’a kashe ma fadar shugaban kasa Naira Biliyan 3.9
Duk da cewa ana ta faman fadin cewa Najeriya bata da Mai, Gwamnatin Tarayya na shirin kashe ma fadar shugaban kasa wadannan kudaden.
9. Kacikwu ya bayyana cewa Najeriy ta kashe Naira Tiriliyan 5 akan tallafin Mai a cikin shekaru 5
Karamin Ministan Mai ya bayyana cewa Najeriya duka Yammacin Afirika take ba Tallafin Mai. Kuma a cikin shekaru 5, Najeriya ta kashe kimanin Naira Tiriliyan 5 akan tallafin.
10. Rochas yayi ma mai’aikin shi babban biki
Bayan tayi shekaru sama da 20 tana yima iyalin shi hidima, Gwamna ROchas yayi ma mai’aikin shi wani biki babba.
The post Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).