Yadda yan Najeriya sun yi butulci ni – Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
– Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana maganta kan ra’yinsa game da al’ummar Najeriya
– Dakta Jonathan bashi farin ciki yadda wasu yan Najeriya suke cewa kan gwamnatinshi inda yake yi mulki
Rahotanni na nuna cewa wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yace wanda, yan Najeriya sun yi ma shi butulci.
Wani tsohon shugaban kasar Najeriya daga 2010 zyuwa ga 2015
Dakta Goodluck Jonathan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda akasarin yan Najeriya suka yi masa butulci duk da sadaukarwar da ya yi wa wannan kasa.
KU KARANTA KUMA: Yaki da rashawa: John Onaiyekan ya shawarci Shugaba Buhari
Tsohon shugaban ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake mayar da martani kan rahoton cewa yana gudun mafaka a Kwaddibuwa inda ya nuna cewa ana yaba masa a kasashen Afrika bisa rawar da ya taka na hana zubar da jini a zaben 2015 amma a Najeriya sai ci gaba da muzanta shi ake yi.
Ya nuna cewa ya ziyarci Kwaddibuwa ne don ya gudanar da hutunsa a can bayan ya kwashe kusan wata guda yana ziyartar wasu biranai a nahiyar Turai inda ya jaddada cewa da zarar ya kammala hutunsa, zai dawo Najeriya.
A jiya, Litinin, 23 ga watan Mayu ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fasa zuwan shi jihar Legas, amma mataimakinsa Yemi Osibanjo ne zai wakilce shi.
The post Yadda yan Najeriya sun yi butulci ni – Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).
