Ramadana: Abubuwa 5 tattare da wannan watan
– Watan Ramadana shine wata mafi nishadi ga Musulumai
– A wannan watan,Musulmai na ayyukan alkhairi tukuru hissi da amali
– Amma ca! watan ya zo karshe,kwanaki kalilan suka rage
Watan Ramadana wata ce mai albarka,watar da ba ta zuwa ta tafi face ta bar alama mai girma a zukatan musulmai. Musulmai na tuna ayyukan ibadu na safe,rana, da dare a cikin watan. Ga wasu riban kafa guda 5 da musulmai zasu samu da tafiyar watan.
- Kajiyan Jiki
Azumin watan Ramadana ta kunshi kamewa daga ci da sha, musulmi zai kwashe sa’o’I da yawa bai dandana komai a harshen sa ba,wannan sai ya kawo gajiyan jikin da zai hanashi aikata wasu abubuwan da bai kamata ba. Kana likitocin kimiya sun tabbatar da cewa,kamewa da ci ko sha na sa’o’I na da amfani ga jikin dan Adam. A Najeriya,musulmai na kwashe akalla sa’a 14 bakuna na rufe, amma a wasu kasashe Kaman kasashen turawa, suna kwashe sa’a 20 suna azumi.
Wannan yana kawo ragin karfin jiki, amma musulmai suna jurewa suyi azumi a watan gaba daya.
- Farin cikin lokacin buda baki
Idan lokacin buda baki yayi, zaka lura Musulmai na cike da farin ciki da walwala. A lokacin makogoro yayi matukar bushe wa ,kuma gangan jiki na bukatan wani abu.
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yace: Akwai lokuta 2 da mai azumi ke farin ciki. Lokaci na farko shine lokacin buda baki, lokaci na biyu shine ranan da zai hadu da Ubangijin sa. Allah ba mu ikon samun wadanan.
- Izza da himman juriya a watan Ramadana
Shin ta yaya mutum zai yi azumi tun daga safe har faduwar rana kuma ya tashi cikin dare yayi Sallar Tahajjud? Ta yaya mutum zai sha yunwa da kishi kuma ya nace sai ya karanta sura 10 cikin Alkur’ani kullun? Ta yaya mutun zai kame bakin shi,yayi Sallan asham,ya halarci Tafsirin Ramadana,kuma yayi ayyukan shin a yau da kullun?
Amsan shine,wadanna na yiwuwa ne kawai a watan Ramadana
KU KARANTA : Karuwai sunyi makoki a kan rashin ciniki a lokacin Ramadan
- Zaman sauraron wata Ramadana
Kafin watan Ramadana ta zo, Musulmai za suyi ta daukin zuwanta, idan tazo komai canzawa za ke yi. Kai,ni’ima da irin wannan wata.
- Raguwan Laifuffuka
Da Zuwan watan Ramadana, Mazinaci zai daina,Makaryaci zai rage,Marowaci zai fara sadaka,Barawo zai ji tsoron Allah, Masallatai suna fara cika, Gidajen maye na ramewa,kai har yan gidajen magajiya sun shaida. Kuma mafadaci zai ce,ina azumi.
The post Ramadana: Abubuwa 5 tattare da wannan watan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.