Buhari ya karbi bakoncin mambobin sojojin diflomasiyya
-Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha ruwa tare da mambobin diflomasiyya a fadar sa ta shugabanci
-Shugaban kasa yayi Magana a kan yan’bindigan Niger Delta, yan’taaddan Boko Haram, ceton matan Chibok
-Ya jaddada kudunrin yanta dukan kamamun Boko Haram da kuma sadar da su ga gidajensu lafiya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin mambobin sojojin diflomasiyya don bude bakin azumin Ramadan a fadar sa a ranar Litinin 30 ga watan Yuni.
A yayin da yake bayani ga bakin nasa, shugaban kasa ya kuma bayyana kudurinsa na ceto sauran yan matan Chibok da aka sace. Ya bayyana cewa babban burinsa shine ya ceto matan a raye kuma cikin koshin lafiya. “Bazamu bar kokarinmu na ganin mun ceton yan’matan Chibok ya tafi a banza ba, burinmu shine mu ceto su a raye cikin koshin lafiya.”
Shugaban kasa Buhari ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da magance matsalar tsaro, tare da cewa ayyukan yan Boko Haram ya mayar da yan’najeriya da dama marayu da kuma marasa galihu.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya yaba ma sojojin Najeriya kan kokarin su
Da yayi Magana a kan yawan kai harin a yankin Niger Delta, shugaban kasa y aba da tabbacin cewa an magance matsalar. Duk da haka, Buhari ya tabbatar da cewa “babu yawan yan’bindiga da zai hana mu mu’ammala da yankin”.
A cewar shugaban kasa, gwamnatinsa tana aiki dan ganin cewa ta magance matsalar rashin aikin yi, rashin ababen more rayuwa, da kuma matsalolin muhalli: “kofofinmu na bude dan harkokin kasuwanci.”
The post Buhari ya karbi bakoncin mambobin sojojin diflomasiyya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.