Babban kotun tarayya ta mara ma Ali Modu Sherrif baya
-Wata babban kotun tarayyan da ke zaune a babban birnin tarayya Abuja, ta bada wani fatawan da ke wajabta ma INEC, PDP ko wani ma’aikaci biyayya ga kwamitin karakashin shugabancin Sherrif.
-Alkali mai shari’ar da yanken wannan hukuncin, Jastis Okon Abang, yace doka bata amince PDP, INEC ta gana da kowane jama’a ba face kwamitin Sherrif.
-Mai Shari’ar ya kare da cewa jama’a suyi watsi da kowani taron da ba Sherrif ya shirya ba
Ali Modu Sheriff
Hayaniyar shugabancin da ke gudana a jam’iyya adawa ta PDP ta dau sabuwar lale a ranan Alhamis,30 ga wata yuni yayinda wata babban kotun tarayya da ke zaune a Abuja ta hana hukumar gudanar da zabe na kasa mai zaman kanta INEC amincewa da kowani jerin sunayen ‘yan takaran gwamna karkashin jam’iyyar PDP, sai na kwamitin Ali Modu Sherrif.
Game da Jaridar The Nation, kotun ta hana INEC, PDP, ko wani ma’aikacinta ganawa da kowani jama’a akan zaben firamaren Jihar Edo da Ondo face shugabancin Sherrif, Sakataren sa Farfesa Wale Oladipo da Fatai Adeyanju.
Alkali mai Shari’a , Jastis Okon Abang ya yanke hukuncin da ke wajabta ma INEC da PDP hada dai da kwamitin sherrif kamar yadd doka ya tsara. Kana kotun ta hana inec da pdp shirya wani taro ko zaben firamaren da ba kwamitin da Sherrif ya nada suka shirya ba.
KU KARANTA : Ogah ba zai zama gwamna ba, mun shirya mutuwa- PDP
Baya ga da haka, PDP ta yi watsi da labarun da ke yaduwa a kafafun yada labarai cewa wata babban kotun da ke zaune a babban birnin tarayya abuja, ta kori shugaban jam’iyyar ta PDP, Ali modu Sherrif.
A wata jawabin da sakataren jam’iyyar PDP ta kasa, Farfesa Wale Oladipo, ya sa hannu, jam’iyyar PDP tace rahoton karya ce , anyi mumunan fahimtan hukuncin da kotun ta yanke ne. Farfesa Wale Oladipo yace: “Kotu ba ta yanke hukuncin koran shugaban jam’iyya ta kasa ba.” Ya ce innama kotun ta yanke hukuncin ne bisa gyaran kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ne kawai.
The post Babban kotun tarayya ta mara ma Ali Modu Sherrif baya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
