Sojoji sun kai hari ga yan’ta’addan dake neman tserewa
-An kasha wasu mayakan Boko Haram a wani hari da sojoji suka kai ga yan’ta’adda a Kangarwa
-Sojoji 8 da yan farar hular JTF 2 ne suka samu rauni a lokacin fama da maharan suna kuma samun kulawan likita tun a lokacin
-Wasu daga cikin abubuwan da suka karbo daga yan’ta’addan ya hada da motoci, bindigan General Purpose Machine Gun (GPMG) guda 1, AK-34 guda 3, Bam 6 da sauran su
Mayakan Boko Haram sun kuma shan kaye a hannun sojojin Najeriya, bayan dakarun sun farma yan ta’addan dake tsere daga kasashen makwabta.
A wata sanarwa daga darakta sojojin, yan ta’addan Boko Haram da dama sun rasa rayyukan su a yayain da wasu da dama suka tsere tare da raunukan harbin bindiga, a Kangarwa, a yammacin, ranar Laraba 29 ga watan Yuni.
KU KARANTA KUMA: Karuwai sunyi makoki a kan rashin ciniki a lokacin Ramadan
Usman ya bayyana cewa, sojoji 8 da yan farar hulan JTF 2 ne suka samu rauni a lokacin fama da maharan kuma tun daga lokacin suke samun cikakken kulawan likita, kuma ana samun nasara kan warke wan ciwon.
Kakakin sojojin ya bayyana cewa a lokacin faman, an harba wani Rocket Propelled Grenade (RPG) a tankar mai da kuma wasu wayoyin lantarki, motar wani daga cikin sojojin ya kama da wuta, amma sojan ya kasha wutan da sauri.
A halin yanzu, Shugaban kasa Muhmmadu Buhari ya ce gwamnatin sa zata gyara kasar Najeriya, tare da yankin Niger Delta.
Wannan na cikin wani jawabi da Femi Adesina, mai ba shugaban kasa shawara yayi a kafofin yada labarai a jiya, 30 ga watan yuni.
The post Sojoji sun kai hari ga yan’ta’addan dake neman tserewa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
