Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Zlatan Ibrahimovic zai koma Kungiyar Manchester United

0

Zlatan Ibrahimovic ya tabbatar da cewa zai koma Kungiyar Manchester United

– Shahararren Dan wasa Zlatan Ibrahimovic, zai koma Kungiyar Manchester United a Kakar bana da taka leda.

– Kwantiragin dan wasa Ibrahimovic da Kungiyar PSG na Faransa ya kare, zai koma Kasar Ingila da wasa.

– Zlatan Ibrahimovic zai rattaba hannu kan yarjejeniyar Shekara daya da Kungiyar Manchester United.

Fitaccen Dan wasan gaban nan, Zlatan Ibrahimovic ya sanar ta shafin sa na Instagram cewa zai koma Kungiyar Kwallon Kafar Manchester United ta Kasar Ingila da buga wasa. Dan wasan mai shekaru 34 a duniya ya zama ba shi da kulob bayan da kwatiragin sa da Kungiyar PSG ta Kasar Faransa ya kare a ranar Alhamis, bayan hakan ne Dan wasan ya sanar da cewa zai koma Kungiyar Manchester United. Ya rubuta a shafin san a Instagram; “Lokaci yayi da ya kamata duniya ta sani, daga nan kuma sai @manchesterunited (watau dai Kungiyar Manchester United) #iamcoming (Watau Gani nan tafe)

 

 

 

 

 

Gidan talabijin din wasanni na ESPN sun ce, Lokacin da dan wasa Zlatan Ibrahimovic yayi wannan magana a yanar gizo, bai saka hannun wata yarjejeniya da Kungiya Manchester United ba tukun, kuma ma dai har yau ba su duba lafiyar jikin sa ba, bari ma dai Kungiyar ta Manchester United ba ta tabbatar da wannan magana na Zlatan Ibrahimovic din ba kawo yanzu haka. Amma dai wata majiyar ta nuna cewa ya saka hannu cikin wata yarjejeniyar shekara guda da Kungiyar ta Manchester a wancan makon, sai dai wani sharadi da ke cikin yarjejeniyar sa da Kungiyar PSG a wancan lokaci ya hana abun ya tabbata. Kungiyar Manchester United dai ta ce za ta buga wani wasa da Kungiyar Galatasaray na Turkiyya a Kasar su Zlatan Ibrahimovic, Sweeden a ranar 30 ga watan Yuli.

Idan ana so a sha labarai, sai a sauke manhajar mu ta NAIJ.com

The post Zlatan Ibrahimovic zai koma Kungiyar Manchester United appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *