Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Buhari zai kaddamar da ayyukan kudu maso kudu–Jigon APC

0

–     Ana sa ran Shugaba Buhari zai kaddamar da ayyukan da zai ma yankin kudu maso kudu kafin karshen wannan shekaran.

 –    Ana sa ran ya kaddamar da aikin jirgin kasa Legas zuwa kalaba

–     Wani jigon APC a yankin ya ce Shugaban kasan zai cika alkawuran sa.

 

Ana kyautata zaton Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari zai kaddamar da manyan ayyuka a yankin kudu maso kudu musamman Jihohin Kross Riba da Akwa Ibom, kafin karshen wannan shekarar.

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa an samu hakan ne daga bakin mataimakin Shugaban jam’iyyar APC ta kasa a yankin kudu maso kudu, Ntufam Hilliard Eta.

Eta yace : “Ina da masaniyar cewa Shugaban Kasa ya ambaci yadda zai kawo ayyuka da yawa yankin kudu maso kudancin najeriya saboda akwai kwan zinariyar da akeyi a yankin. Bari ma, akwai wani babban aiki musamman da zai fara gudana a kalaba.

Yace gwamnatin tarayya zata iya kaddamar da aikin jirgin kasan legas zuwa kalaba sabanin surutan da wasu ke yi akan aikin. Ya nuna kyakkyawan zaton sa ga gwamnati na gyaran hanyar titin motar itu zuwa kalaba, wannan hanyan ne da ya yi shekaru a lalace. Yankin ta Kudu maso Kudu dai na fuskantar kalubale da dama, yayinda wasu sabbin yan bindiga masu suna Niger Delta Avengers na daukan alhakin sanya wa kafufuwan man fetur bam.

KU KARANTA : Tsagerun Nija Delta sun bude wuta a Ogun

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki yan bindigan da sunan Allah da su daina baraka a yankin, kuma ya nada wata kwamitin sulhu karkashin Shugabancin Mai Martaba , Amanyanabo of Twon Brass a jihar bayelsa, King Alfred Diette-Spiff. Yace : “Muna son gyara wannan kasa ta mu saboda yaran mu da jikokin mu suyi alfahari da kasar su. Anyi lalata da yawa, saboda haka ina son ku gaya ma mutanen suyi hakuri. Idan kuka hadu da sauran shugabannin , ina rokon ku da ku lallashe su. Zamuyi amfani da duk arzikin najeriya da tsoron Allah kuma mu gyara kasar nan.

The post Buhari zai kaddamar da ayyukan kudu maso kudu–Jigon APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *