Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Yan Najeriya na kukan hauhawar farashin Kalanzir N220

0

 –   Ana sayar da litan Kalanzir N220 a Jihar Legas sabanin N50 da Gwamnati ta sa

 –   Wasu yan najeriya sun ce su basu ga canjin da suka kada wa kuri’a ba, saboda wahala suke ci.

Sanadiyar kalubalen da tattalin arzikin kasa ke fuskanta, farashin Kalanzir ya tashi zuwa N220 sabanin N50 da Gwamnati ta ce a sayar.

ana jiran layin kalanzir

Game da Jaridar Daily Sun, yan Najeriya na kokawa game da mawuyacin wahalan da suke sha Sanadiyar tashin kudin Kalanzir.  Wata ‘yar kasuwa, Funmi Olayokun, tace tashin kudin kalanzir zuwa N220 ba karamin halin kakanikaye zai sa talakawa ba, saboda dogaron su ga kalanzir domin tasarrufi. Funmi Olayokun mai yara 5 tace abin bai mata dadi ba, ta ce halin da Najeriya ke ciki , ba canji da suka zaba ba kenan. Ta kara da cewa kudin kayayyakin abinci sun tashi ninki biyu , yan najeriya bacci suke da yunwa.

Wani Direban mota mai suna Seun Busari yayi Allah wadai da kungiyar kwadago ,yace : “Yan kungiyar kwadago da yan najeriya suka dogara da su sun sayar da yancin su.” 

Onyemaechi Ukaegbu, wani masanin na’urar komfyuta, ya sanya wa yan najeriya laifin abinda da ke faruwa. Yace idan mutane na saban Ubangiji, zai sa azzalumi ya shugabance su. Abinda ke faruwa a najeriya kenan , yanzu ma wahalan ya fara. sai yan najeriya sha wuyan zaben canji.

KU KARANTA : An gwada Jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna

Ku tuna cewa watanni 4 da suka gabata , an sayar da litan kalanzir N115 zuwa N120 a jihar akwa ibom , a fatakwal kuma N100 zuwa N150, amma a babban birnin tarayya, an sayar N140 zuwa N150.   Direktan Action Aid, Ms. OJOBO Atukuku, ta ce shawaran gwamnatin tarayya na cire tallafi akan kalanzir na nuna cigaba da samarwan wannan gwamnatin da ke gallaza ma mutane a wannan kwanakin.

The post Yan Najeriya na kukan hauhawar farashin Kalanzir N220 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *