Gwamna Yahaya Bello yayi cirko-cirko a Jihar Kano
– Gwamnan Jihar Kogi Abubakar Yahaya Bello ya cikaa baban filin jirgin saman Aminu kan international a Jihar Kano ta dalilin esfiyan bizan sa na zuwa kasa mai tsarki domin aikin Umra
– Sai ya karasa gidan Gwamnatin Jihar Kano ,inda ya kwana.
Gwamna Yahaya Bello a kasar saudiyya
Wannan matashin Gwamnan Jihar Kogi Abubakar Yahaya Bello yayi cirko-cirko a Jihar Kano ,yayinda ya je babban filin jirgin saman Aminu kano domin zuwa kasa mai tsarki,Kasar Saudiyya ,domin gabatar da aikin Umra cikin watan Ramadana. Ashe bizan sa ta mutu.
Game da Gidan Jaridar Sahara Reporters, gwamnan ya hau wata jirgin da ke tafiya kasar Saudiyya da yammacin ranar Laraba.29 ga watan yuni, yana zaune ana shirya masa takardun tafiya kawai sai aka lura cewa bizan sa tayi esfiya.
Da aka sanar da Gwamnan cewa bizansa tayi esfiya,abun bata masa dadi ba. Amma yaya zai yi? Sai ya dau na annabawa yayi hakuri,ya sauka daga cikin jirgin. Sai ya karasa gidan gwamnatin jihar kano ,inda ya kwana.
KU KARANTA : Mutane 2 da Suka Gudu daga gidan Yarin Kuje.
A bangare daya, hayaniyar shugabancin da ke faruwa a majalisar Jihar Kogi zai yi sauki yanzu,tunda bangarorin hammayan guda 2 sun amince ayi sulhu,kuma a zauna lafiya da juna . Hakan ya faru ne yayinda gwamnan jihar kogi yahaya bello,da mataimakin sa,Simon Achuba,da wasu manyan ma’aikatan gwamnatin suka gana da bangarorin hamayyan. Jaridar This Day ta bada rahoto.
Bayan ganawar ranan Alhamis,23 ga watan yuni, an nada wata kwamitin mutane 10 domin tabbaar da zaman lafiya a majalisan.
The post Gwamna Yahaya Bello yayi cirko-cirko a Jihar Kano appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.