Wasa Euro2016: Portugal ta kai zagaye na 2
Dan wasa Ricardo Quaresma shi ya zama gwarzon jiya inda ya kutsa da Kasar Portugal zuwa zagaye na gaba a Gasar EURO na wannan shekarar.
Quaresma ne ya buga finaritin da ya tabbatar cewa Kasar Portugal ta buge Kasar Poland zuwa zagaye na kusa da Karshe a Gasar Kwallon Kafar zakarun Turai watau EURO 2016 da ake bugawa a Faransa. An dai tashi wasan ne kunnen doki kafin Kasar Portugal tayi nasara a bugun finariti (bugun daga kai-sai mai tsaron gida) da ci 5-3.
Jakub Blaszczykowski na Kasar Poland ya zubar da na sa finaritin inda Golan Kasar Portugal, Rui Patricio ya tsalle ya buge ta. Sai dai shi kuwa dan wasa Cristiano Ronaldo bai yi wata-wata ba wajen zuba ta sa a cikin ragar Poland. Shi ma dan wasa Robert Lewandowski na Poland ya buga finariti mai kyau, sai dai Rui Patricio ya gan ta cikin zare. Blaszczykowski ne dai ya samu matsala wajen na sa bugun. Yanzu haka Kasar Portugal ce ta fara zuwa zagaye na kusa da karshe a gasar na EURO 2016.
Kasar Poland: Lukasz Fabianski (Gola); Lukasz Piszczek, Kamil Glik, Michal Pazdan, Artur Jedrzejczyk; Jakub Blaszczykowski, Grzegorz Krychowiak, Krzysztof Maczynski, Kamil Grosicki; Arkadiusz Milik; Robert Lewandowski (Kyaftin) Mai horo: Adam Nawalka.
Kasar Portugal: Rui Patricio (Gola); Cedric Soares, Pepe, Jose Fonte, Eliseu; Renato Sanches, William Carvalho, Adrien Silva, Joao Mario; Cristiano Ronaldo (Kyaftin), Nani Mai horo: Fernando Santos.
Duka kasashen sun buga tsarin 4-4-2 inda alkalin wasan shine Felix Brych dan Kasar Jamus. An tashi 1-1 har bayan Karin lokaci. Inda aka buga 5-3 a finariti, Portugal tayi nasara bisa Poland. Ricardo Quaresma wanda ya shigo daga baya, ya canji Joao Mario shi ya ci finaritin Karshe a wasar, ko a baya dai ya ci ma Kasar Portugal kwallo a Gasar.
The post Wasa Euro2016: Portugal ta kai zagaye na 2 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.