Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Manyan laifuka 6 da ake aikatawa a Najeriya

0

-Hukumar hana yima tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC a takaice na  da zarra wajen zakulo masu laifi ta kuma gurfanar dasu gaban shari’a 

-Haka kuma hukumar tayi tasiri wajen fadakar da ‘yan Najeriya game da illar cin hanci da rashawa, da kuma yadda za’a iya kauracema laifin

efcc

Hukumar EFCC ta zayyana manyan laifikkan wadanda suka zamar ma kasar karfen kafa wajen ci gaban tattalin arziki. Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu yana yima hukumar kwaskwarima domin mayar da hukumar zama wadda ta dauki nauyin da ke kanta ta muhimmanci.

Wadannan laifuka sune kamar haka:

  1. Laifin tattalin arziki

Laifin daya shafi tattalin arziki.

Laifin ya shafi gurguntar da arzikin gwamnatin jiha ko ta tarayya. Ya jibanci laifuka irin su fasa bututun mai, satar mai, kin biyan haraji da sauransu.

  1. Laifukkan da suka Shafi kudi

Wannan laifikkan sun shafi amfani da kudi ba bisa ka’ida ba ko kuma abubuwa da suka danganci haka, irin su cekin kudi, cekin draft, bada ceki na karya da sauransu.

  1. Zamba cikin aminci

Ya shafi yaudara da niyyar cuta ta hanyar amsar kudi domin wata sabgar kasuwanci, ko soyayyya ko kwangila da sauransu.

  1. Halarta haramtattun kudade

Shigar da haramtattun kudade cikin sabgar kasuwanci yadda zasu kasance kamar an wankesu.

  1. Ta’addanci

Amfani da tashin hankali, taratsi da barazana domin cima wani guri na siyasa, ko addini ko manufa.

  1. Laifukkan yanar gizo

Sun shafi amfani da na’ura mai kwakwalwa ko kwatankwacin haka domin yin laifi

Shagunan da ake shiga yanar gizo dole su yi rajista da EFCC domin su san abinda suke cike, su kuma kaucema laifikkan yanar gizo.

KU KARANTA:Kotu ta garkame tsohon gwamna a kurkukun Kuje

 

The post Manyan laifuka 6 da ake aikatawa a Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *