Shin Aisha Buhari ta shirya ziyartan Amurka?
-Aisha Buhari ta bar kasar Najeriya domin yin Umurah a sakar Saudiya
-Tafiyar nata ya janyo jita-jitan cewa matar shugaban kasa ta soke tafiyar ta zuwa kasar Amurka saboda zargin da akayi na cewa tana cikin abin kunyan Halliburton
Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta kasance cikin wani sabani da gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose kan zargin aikata cin hanci da rashawa. Ya bayyana cewa matar shugaban kasa, Aisha Buhari taki zuwa kasar Amurka domin tana tsoron kar a kamata.
KU KARANTA KUMA: Kyawawan sabon hotunan yar mataimakin gwamnan Fulato
Bayan zargin nasa, wasu yan Najeriya sun yi kira ga matar shugaban kasa, cewa ta je kasar Amurka domin tabbatar da gaskiyanta. Daga baya, labari ya fito cewa matar shugaban kasa ta shirya ziyartan kasar Amurka domin hallartan taron matayen shugabannin kasa na duniya, wanda za’ayi a Colorado. A yanzu haka, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, matar sugaban kasa Buhari, ta bar kasar Najeriya domin yin aikin umurah a kasar Saudiya.
Aisha Buhari
Daraktan labarai na ofishin matar shugaban kasa, Zakari Nadabo ya bayyana haka a wani sanarwa, a ranar Ltinin 30 ga watan Yuni. Amma bai fadi komai game da soke tafiyar ta zuwa kasar Amurka ba.
The post Shin Aisha Buhari ta shirya ziyartan Amurka? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
