Fadar Shugaban kasa ta nemi gafarar Majalisa dattawa
– Majalisar Dattawa ta gayyaci Babban Lauyan tarayya kuma Ministan Shari’a ,Abubakar Malami, domin ya amsa tambayoyi bisa aikin jabun dokokin da akayi
– Mai ba Shugaban kasa shawara akan la’anta, Okoi Obla ne ya wakilce shi.
– Majalisar Dattawa ta fitittike Mai ba shugaban kasa shawara akan la’anta, Okoi Obla, daga cikin majalisa a ranar Alhamis, 30 ga watan yuni.
shugaba muhammadu buhari da saraki
Fadar Shugaban kasa ta nemi gafarar Majalisa dattawa a bisa maganan da wakilin babban lauyan tarayya ya yi a ganawar sa da kwamitin shari’a da hakkin dan Adam.
Mai baiwa shugaban kasa shawara akan abubuwan da suka shafi bangaren dokokin na majalisa dattawa, Ita Enang, ne ya bada hakurin yayinda yake magana da manema labarai a Abuja , a ranar juma’a. Ita Enang Ya ce : “Wakilin babban lauyan tarayya, Okoi Obla yayi kuskure yayinda yace majalisar dattawa ba ta da hurumin gayyatar babban lauyan tarayya, Abubakar Malami. Na ji maganganun daga baya shi yasa nike son in nemi gafarar majalisa dattawa da kwamitin doka, da kuma Senatocin gaba daya. Bai kamace shi ya furta wannan maganan ba, babban lauyan kasa, shugaban kasa ne ya nada shi, kuma majalisa ce ta tantance shi, domin haka dan kasa ne. Za mu sake koma cikin maganan, za mu yi dubi a ciki amma bari in fara bada hakuri ga Majalisa , Senatoci da mambobin kwamitin.”
KU KARANTA : Bita da kulli ake mana-Majalisar Dattijai
Majalisar Dattawa ta gayyaci babban lauyan tarayya ne akan karar yan majalisan da ya kai a bisa aikin jabun dokokin majalisa. Amma, babban lauyan tarayya bai amsa gayyatar ba, ya tura mai ba Shugaban kasa shawara akan la’anta, okoi obla, ya wakilce shi. Duk da cewan kwamitin ta ki sauraron wakilin babban lauyan tarayya, Mr Obla ya fadawa manema labarai a wajen dakin ganarwa cewa “ Majalisa dattawa ba ta da hurumin gayyatar babban lauyan tarayya”
Amma , Mr Ita Enang ya bada hakuri a madadin babban lauyan tarayyan domin baya nan.
“Babban lauyan tarayya yayi magana da ni da safe cewa yanada aikin yi, idan ya dawo , zamu shirya yanda za’ayi, amma kafin nan muna bada hakuri.”
The post Fadar Shugaban kasa ta nemi gafarar Majalisa dattawa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.