Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Watford ta Sayi Dan wasan Najeriya

0

Kungiya kwallon kafa ta Watford ta sayi dan wasan gaba kuma dan Najeriya Isaac daga kungiyar Granada.

Cinikin ya kammalu ne tun watan Janairu amma ba’a bayyana ba, dana wasan ya samu tayi daga kungiyoyi da dama daga ciki har da Atletico Madrid, Inter Milan da kuma PSG, Watford ta saye shi ne akan kudi pan miliyan 12 da dubu 500,000.

Isaac a Granada

Tun a farkon shekarar nan ne aka cin ma yarjejniyar, sai dai dukkan bagarorin sun amince kada a sanar har sai karshen kakar wasa saboda Granada tana cikin tataburzan fadawa rukunin wasa na kasa da laliga. An danganta dan shekaru 20 da wasu kulob dake nahiyar Turai ciki har da PSG da Inter Milan, sai dai wakilin Success Dominic Egbukwu tun a watan Fabrairu ya tabbatar da cewa Dan wasan zai koma Watford ne.

Yace “Atletico Madrid, Inter Milan da PSG duk sun neme mu, kungiyoyi da dama sun neme

Shi, sai dai Granada ba su yarda su sake shi ga Valencia ba ko wani kulob na daban ma idan dai ba Watford bane”. Success ya zura kwallaye 5 a wasanni talatin da ya buga a kakar wasa da ya buga La Liga. Ana ganin Success zai shiga gasar neman grubin buga wasa a kungiyar Watford cikin kakar wasa tare da Troy Deeney da kuma dan kasarsa Odion Ighalo, mafi muhimmanci dan wasan gabansu. Kuma dai Watford ta siya Christian Kabasele daga Kungiyar Genk da ke Belgium.

The post Watford ta Sayi Dan wasan Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *