Siasia ya bayyan ya wasa 4 da zasu samu zuwa gasar Olimfik
John Mikel Obi, Daniel Akoeyi, Kenneth Omeruo sun samu shuga jerin yan wasan da zasu samu halartar gasar Olimfik na bana da za’ayi a birnin Rio na Brazil, haka shima Wilfred Ndidi yayi alkawarin tarar Kungiyar kwallon a Amurka kafin a fara gasar.
Samson Siasia ya na da yakinin kungiyar zata iya lashe wasu mukamai a gasar ta 2016. Mai hurar da yan wasa na kasa da shekaru 23 na Najeriya ya bada tabbacin John Mikel Obi, Daniel Akoeyi, Kenneth Omeruo zasu samu halartar gasar Olimfik na 2016 da za’ayi a birnin Rio na Brazil
Siasia ya koka dangane da yadda wasu kungiyoyi basu son sakin yan wasan su don gasar Olimfik din, kaamr Alex Iwobi da Iheancho. Mai horarwan ya bayyana cewa dan wasan tsakiya Wilfred Ndidi zai samesu a Amurka kafin a fara wasannin a watan agusta. “Akwai wasu yan wasan da suka yi alkawarin ishe mu, kuma sun bayyan aniyarsu kamar Wilfred Ndidi wanda ya bamu tabbacin ishe mu a Amurka” in ji shi.
Ya kara da cewa “wasu yan wasan da sukayi alkawarin zuwa sun hada da Mai tsaron raga Daniel Akpeyi, Kenneth Omerou da Mikel Obi. Wadannan sune suka tabbatar mana da zuwansu” in ji Siasia a da yake tsatsatsage bayani ga Goal. “idan zamu samu dukkan yan wasan nan gami da wadanda muke dasu, kuma ace su yi wasa yadda ya kamata, ina da tabbacin zamu samu damar cin zinariyar gasar”, “amma kamar yadda na sha fada, ba abu bane mai sauki, amma zamu yi kokarin shirya wannan kungiyar don ganin sun ciyo kyauta mafi tsoka a gasar”
A wani hannun kuma, Minisan wasanni na Najeriya ya nuna shakkarsa dangane da Mutum 35 da Samson Siasia ya diba don tafiya gasar. Ministan bai ji dadi ba ganin yadda Siasia ya cire yan wasa da dama wadanda suka cancanci zuwa gasar ta hanyar cin gasan yan kasa da 23 na Nahiyar Afrika a watan Disamba ta 205.
The post Siasia ya bayyan ya wasa 4 da zasu samu zuwa gasar Olimfik appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.