Anyi garkuwa da dan diflomasiyyan Siriyalone a Kaduna
– Jihar Kaduna ta fara zama wurin garkuwa da mutane kwanakin nan
– An yi garkuwa da mataimakin jakadan kasar siriya lone zuwa najeriya, Majo Janar Nelson Williams a Jihar.
Majo Janar Nelson Williams Tsohon Shugaban Dakarun Sojin Siriyalone ne
Gwamna Nasir El Rufai jihar Kaduna
Hankalin Jami’an tsaron Najeriya ta tashi yayinda akayi garkuwa da mataimakin jakadan kasar Siriya lone zuwa Najeriya, Majo Janar Nelson Williams a Jihar kaduna. Wannan aiki abin kunya ne ga jami’an tsaron Najeriya, yadda garkuwa da mutane ya fara yawaita a Jihar Kaduna, Arewa maso yammacin Kasa.
Watanni 3 da suka gabata, anyi garkuwa da wani babban hafsan soja, Kanal Samaila, a Jihar. Daga baya aka tsince a mace,Amma an damke makasan. Ba da dadewa ba aka yi garkuwa da wasu shugabannin cocin na kungiyar Kiristocin Najeriya. Kamar dai yadda aka kashe babban hafsan sojan, an tsince gawar shugaban cocin a cikin daji ta fara kumbura.
Hakan yasa ofishin yan sandan Jihar Kaduna ta nada wani tawaga na musamman domin ya ki masu garkuwa da mutane, da kuma dabar yan daba.
KU KARANTA : Yan Najeriya na kukan hauhawar farashin Kalanzir N220
Garkuwa da mataimakin jakadan kasar siriya lone zuwa najeriya, Majo Janar Nelson Williams,babban kalubale ne ga jami’an yan sandan Jihar Kaduna. Anyi garkuwa da Dan diflomasiyyan ne a yau 1 ga watan yuli, bayan ya je halartar taron kammala digirin makarantan Soja. Wasu majiya a ofishin jakadancin Siriyalone a Abuja ta ce yan bindigan sun kira suna bukatan $40 miliyan kudin fansa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarbi wasu yan diflomasiyyan domin buda bakin azumin watan Ramadan a fadar Shugaban Kasa.
The post Anyi garkuwa da dan diflomasiyyan Siriyalone a Kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.