Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Rundunar yan Immigration sun kama yan kasar Benin 40

0

Wasu yan kasar Benin 40 ne rundunar yan Immigration suka kama da katin zaben kasar nan watau Permanent Voters Cards (PVC). 

.

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa Mataimakin shugaban rundunar mai kula da yankin Legas da Ogun Mr Musa Maza ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Maza ya fadi hakan ne a wani taron karramawa da wata kungiyar yan China sukayi yi masa.

A wurin taron nema ya bayyana cewa duka wadan da aka kama din yan Benin ne amma kuma mazauna garin Legas. Ya kuma kara da cewa an kama sune a bodar Seme dake badagry kuma har ma an mika su ga hukumar kasar ta Benin don hukun tawa.

Maza yace: “Wasu jami’an mu sun kama wasu yan yammacin Afirika musamman ma Benin da katin zaben kasar nan har su 40 kuma an kwace duka.” Ma za ya kuma cigaba da bayyana irin nasarorin da hukumar ta samu karkashin sa da ya hada da kamawa tare da mayar da wasu yan kasar Niger har su 380 a watan Mayu.

Haka kuma yace: “311 na yan kasar ta Niger an mayar da su kasar su da kuma wasu 69. Haka ma mun mayar da wasu yan kasashen waje da dama da suka kai 1,171 ta jirgin ruwa a cikin watan Mayu din. “Mun kuma anshi wasu yan Najeriya har guda 380 da aka maido gida daga kasashe da dama sakamakon wasu laifuka.

Maza ya kuma shaida wa yan kasar China din cewar hukumar tasu tana jin dadin yadda take hulda da su musamman ma wajen cinikayya da kasuwanci. Sannan kuma ya tabbatar masu da cewa gwamnatin nan ta shugaba Buhari tana iya bakin kokarin ta wajen tabbatar da yanayi mai kyau don masu zuba jari daga kasashen waje.

The post Rundunar yan Immigration sun kama yan kasar Benin 40 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *