Abu 5 da Faransa zatayi don ta lashe gasar
Duk da cewa ana kyautata zaton mai masaukin baki kasar Faransa ce zata lashe kofin gasar kasahen turan da akeyi a kasar tata amma duk da haka kwallo ba’ayi mata haka don kuwa suma kansu sun san za su iya shan mamaki a hannun kasar Portugal din da shahararren dan wasan ta Cristiano Ronaldo ke jagoranta.
Wasan dai zai sa Cristiano Ronaldo da Antoine Griezmann su sake haduwa a karo na biyu a wasan karshe sati 6 bayan sun buga wasan karshe na zakarun nahiyar turai.
Ga kadan daga cikin abubuwa 5 nan da kasar ta Faransa zatayi don ta lashe gasar:
1. Yin kaffa-kaffa da Ronaldo: ganin yadda dan kwallon yake da matukar muhimmaci ga tawagar kasar sa da kuma matukar hatsari a cikin fili, dole ne ayi kaffa-kaffa da shi.
Duk da cewa dan wasan bai fara gasar ba da kafar dama, amma ya samu cigaba sosai wajen wasan nasa inda ya taimaki kasar tasa a lokuta da dama.
Shi dai Ronaldo zai yi iya baki kokarin sa ya nuna zalamar sa wajen ganin kasar tasa ta samu nasara.
2. Hugo Lloris yayi taka-tsan-tsan da kwallayen sama: duk da kokarin da yakeyi sosai a gasar, mai tsaron gidan Faransa din kuma dan kulob din Tottenham dole ne sai yayi taka tsan-tsan wajen kwallayen sama don kuma yana da matsalar kama su a baya cikin gasar.
3. Hana Raphael Guerreiro zuwa gaba: babu shakka Guerreiro ya taka rawar gani sosai a cikin gasar. Musamman dan wasan na baya yana da gudu sosai inda kuma yaka je gaba yana aika kwallayen cikin gidan gol.
Mai karatu zai iya tuna shi ne ma ya aikama Ronalda kwallon da ya zura a wasan sa na kasar Wales.
4. Yin anfani da magoya baya masu yawa: Ita dai kasar Faransa tana da wata al’ada ta lashe gasar duk da akayi a kasar ta. Ta lashe gasar ta cin kofin kasashen turai a 1984 inda kuma shekaru 16 bayan nan a 2000 suka sake lashe gasar. Haka ma dai a 1998 kasar ta Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar tata.
Yanzu haka dai ana sa ran zata yi anfani da wannan damar tata ta lashe wannan gasar itama.
5. Ragewa Griezmann nauyi: shi dai dan wasan ya zura kwallaye 6 kawo yanzu inda kuma yafi kowa wajen yawan kwallayen da akalla 3. Akwai nauyi da yawa a kan sa a wannan wasan kuma idan ba’a rage masa nauyin ba akwai yiwuwar ya kiyin wani katabus a wasan.
The post Abu 5 da Faransa zatayi don ta lashe gasar appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.