An kushe Ngige domin kare Buhari
–Tunda shugaba buhari ya hau ragamar mulki , ba’a gushe ana kushe shi da bangarenci a wajen nadin mukamai.
–Amma, Ministocin sun kare buhari akan shawarwatin da ya yanke
–A taron da akayi a Jihar Enugu , an yima minista Ngige iwu domin kare nade-naden Buhari.
ministan samar da aikin yi
A ranar 1 ga watan agusta , an yi ma ministan kwadago da tasarrufi, Chris Ngige, iwu a wani taron kudu maso yamma yayinda dake kare shugaba Muhammadu Buhari a nade naden da yakeyi.
Jaridar Daily Post ta bada rahoton cewa shugaban Buhari ya dade yana sauraran kushewan mutane game da nade naden da ya keyi tunda ya hau ragamar mulki a 2015 saboda suna tunani ana sharesu. Jihohin kudu maso gabas, Wadanda basu da kowa a cikin shugabannin tsaro kasa ,sun cigaba da kukunai akan haka.
Zancen bangarencin ne ya zama abin magana a taron tattaunawa a gwamnatin tarayya ta shirya a Nike Lake Resort, Enugu.
KU KARANTA : Manajan Banki ya kashe kansa kan bashin naira miliyan 350
Hakazalika, kungiyar gamayyar yan kabilar Igbo sun bayyana cewan bazasu yarda da wani motsi na tsige mataimakin shugaban majalisan dattawa, Ike Ekweremadu. Yayinda Ngige ke kokarin kare shugaba Buhari , mutanen na yi masa iwun Aaaaaaaa.
Misali yace shugaban ma’aikatan gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi da Nsukka ne, amma mutanen yankin sunce dan Abiya ne ba Nsukka ba.
The post An kushe Ngige domin kare Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
