Zamuyi taron gangamin PDP kamar yadda aka shirya – Wike
– Gwamnan Jihar Ribas nyesome wike yace shirin taron kasa gaba dayan da jam’iyyar PDP ta shirya a ranar 17 ga watan agusta a birnin fatakwal zai yiwu kaman yadda aka shirya.
– Ya kara da cewan shugabannin PDP da ke yankin kudu zasu gana domin tattauna yadda za’a raba mukamai.
Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike yace shirin taron kasa gaba dayan da jam’iyyar PDP ta shirya a ranar 17 ga watan agusta a birnin fatakwal zai yiwu kaman yadda aka shirya. Wike yace Kotu batayi kira akan karar da cirarren shugaban jam’iyyar Ali Modu Sherrif yayi ba akan taron . Ya fadi hakan yayinda yake magana da shugabannin PDP shiyar yankin iudu maso kudu a gidan gwamnati da ke fatakwal a ranan litinin.
Governor Nyesom Wike
“Kotu bazata iya cire sanata makarfi ba saboda bazata iya watsi da daukaka karan da akayi zuwa kotu mai karfi daya da nata ba ,” Wike yace. Gwamnan yafe shiyar jam’iyyar PDP na jihar Edo zata samu goyon baya domin samun nasara akan zaben gwamnan da za’a gudanar.
“PDP a yankin kudu bazata cika ba sai mun kwato Jihar Edo . saboda haka , ina kira fa INEC ta gudanar da zabe na gaskiya a Jihar Edo da wadu jihohin da za’a gudanar da zabe. Ina nuna godiya ta jam’iyyar a jihar edo da kokarinsu wajen yakin neman zabe.”
A matsayin su na jam’iyyar adawa, su kara bunkasa rabon jam’iyyar ta yakin neman zabe mai kyau. Yace . Wike ya kara da cewa shugabannin PDP da ke yankin kudu zasu gana domin tattauna yadda za’a raba mukamai. Gwamnan yace PDP zata kara karfi bayan fitowan ta daga cikin kalubalen da take fuskanta a yanzu, kuma yan najeriya na jiran jam’iyyar da zata bada shugabanci.
KU KARANTA : Kotu ta rushe taron gangamin jam’iyyar PDP
A bangare guda, kwamishanan yada labarai na jihar ribas ,Dr. Austin Tam George yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta watsar da Hukumar INEC karkashin jagorancin Farfesa Mahmoud Yakubu.
The post Zamuyi taron gangamin PDP kamar yadda aka shirya – Wike appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
