Добавить новость
smi24.net
World News in Dutch
Август
2016

Jibrin ya kai karar Dogara hukumar EFCC

0

Biyo bayan yanke shawarar da dan majalisa Abdulmuminu Jibrin ya yi na kai karar kaakakin majalisar wakilai Yakubu Gogara hukumomin tsaro, a jiya Litinin 1 ga watan agusta ya kai karar kaakakin hukumar yaki da zamba da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.

Bayan kwashe awanni biyu a da yayi a babban ofishin jami’an tsaro na sirri, Jibrin ya isa ofishin EFCC dake Wuse 2 da misalign karfe 2.44 na rana. Sai dai isar ofishin ked a wuya aka bukaci yan jaridu da su fita, kuma su jira a wajen kofar shiga ofishin.

Daya daga cikin jami’an hukumar ne ya umarci yan jaridu da su fita, yace “yan jaridu su fita waje.” Da jibrin ya ji haka, shima sai yace “dan Allah idan baka cikin tawaga ta, ka fita waje. Nagode.”

Duk kokarin da mukayi na jin ta bakin mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwajeren ya ci tura, saboda yaki daukan kiraye kirayen da muka masa.

Jibrin ya isa ofishin ne don ganawa da shugabanta Ibrahim Magu, ana tsammanin zai mika takardan koke akan Dogara ga EFCC. Tsohon shugaban kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar wakilai yana zargin Dogara da tare da wasu mutum 9 da laifin kara kudi fiye da naira biliyan 40 a cikin kasafin kudi na shekara 2016. Sa’annan ya nuna a shirye yake ya tunkari duk wani kalubalen shari’a ko kotu da zai iya fuskanta.

The post Jibrin ya kai karar Dogara hukumar EFCC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.















Музыкальные новости






















СМИ24.net — правдивые новости, непрерывно 24/7 на русском языке с ежеминутным обновлением *