Man City sun saye wani dan Schalke 04
Kungiyar kwallon kafa ta Man city sun kammala cinikin dan wasan gefen nan na Schalke 04 dake kasar Germany Leroy Sane har na tsawon shekaru 5.
Su dai Man city din sun sayi Sane ne a kan zunzurutun kudi har £42m. Dan wasan dai ya taso ne tun yana yaro a kungiyar ta Shalke kafin daga bisani ya samu cigaba ya ya zuwa cikin tawagar yan wasan kungiyar ajin farko. Haka ma dai a kakar wasannin da ta gabata dan wasan ya zura kwallaye 13 a cikin wasanni 57 da ya bugawa kungiyar tasa sannan kuma kasar sa ta Germany ta je dashi gasar cin kofin kasashen turai da akayi a kasar Faransa.
A cewar sa: “Tabbas na ji dadi sosai da na dawo kungiyar Man city. Yanzu sai in natsu in zauna a garin na Manchester sannan kuma in yi iya bakin kokari na wajen ci gaban kungiyar baki daya. “Daya daga cikin dalilan da yasa na zo Man city shine mai horarwar kungiyar. Mai horarwar Pep Guardiola shine ya gamsar dani cewar idan nazo nan kungiyar zan ci gaba da shahara duniya ta sanni.”
“Ina bibiyar mai horarwar tun lokacin da yake Barcelona har zuwan sa Baryen, ina lura da yadda yake anfani da matasa masu tasowa sosai”.
Baba Rahman has moved to Germany
A wani labarin kuma mai kama da wannin, kungiyar Shalcke ta bayyana siyan dan wasan bayan Chelsea Baba Rahman a matsayin dan aro. Shi dai Rahman wanda yake da shekaru 22 ya zo Chelsea ne daga kungiyar Augsburg a shekarar da ta gabata a kan kudi £21.7m amma har yanzu bai samu nasarar samun gurbin buga wasa ba na din-din-din a kungiyar.
The post Man City sun saye wani dan Schalke 04 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
