Gareth Bale ya kama hayar wani tsibiri domin neman aure
– Dan wasa Gareth Bale ya bayyana muradin sa ga budurwar sa.
– Dan wasan na Kasar Wales ya kama hayar wani tsibiri ne a Kasar Spain domin ya bayyanawa budurwar Sa abin da ke cikin zuciyar Sa.
– Dan wasan yayi amfani da wannan damar domin taya kan sa murnar cika shekaru 27.
Dan wasan gaban Real Madrid Gareth Bale ya kama hayar wani dan tafki a Kasar Spain domin samun isasshen lokaci don tambayar Budurwar Sa ko za ta aure sa. Dan wasan dai ya bayyana ma budurwar Sa, Emma Rhys-Jones wanda su ka dade tare abin da ke cikin zuciyar sa. Jaridar Telegraph ta Kasar UK ta bayyana cewa Tauraron dan wasan ya kama hayar wani makeken tsibiri mai suna TAGOMAGO wanda ke mita 900 da yankin Ibiza, ko kuma ace kilomita 79 da gabar tekun Valencia, don kawai ya bayyanawa budurwar sa abin da ke cikin zuciyar sa. Dan wasa Gareth Bale ya hadu da budurwar ta sa Rhys-Jones tun suna makaranta.
KU KARANTA: ARSENAL; DAN WASA CHAMBERLAIN YA CI KWALLO A WASA
Kamar dai ya yadda bayanai suka nuna, ana kama hayar tsibirin na TAGOMAGO ne a kan kudi £100,000 kowace rana, haka Gareth Bale ya jibge makudan kudi domin hayar wannan wuri na shakatawar musamman. Gareth Bale ya rubuta a shafin sa na twitter mai lamba @GarethBale11 cewa budurwar ta sa ta amince ta aure sa. Gareth Bale ya rubuta:
Ta ce Eh, Ni ta za ta aura. Ba zan taba mantawa da wannan ranar ba, na lokaci mai tsawo. pic.twitter.com/FQWSiLbLGU
— Gareth Bale (@GarethBale11) Ranar Yuli 17, 2016
Ana kama hayar wannan wuri ne kan kudi €500,000 a mako, akwai katafaran dakuna kusan biyar cikin tsibirin, har da wurin saukar jirgin sama, wannan wuri dai na da girmar eka kusan 100. Gareth Bale dai da budurwar Sa, sun shafe shekaru da dama tare, suna da ‘yaya har biyu; Alba Violet da Nava Valentina.
The post Gareth Bale ya kama hayar wani tsibiri domin neman aure appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.