Ya rasa ransa sanadiyar wutan lantarki
–Makwabci ya tabbatar da mutuwan wani mutun mai shekaru 65 da haihuwa mai suna Adeyemi Ogunleye.
–Tashin hankali ya farune a unguwar Oyemekun a Jihar Ondo , bayan Adeyemi Ogunleye ya rasa ransa sanadiyar wutan lantarki.
Wani dan shekaru 65 mai suna Adeyemi Ogunleye ya rasa rayuwarsa ne a karshen wannan mako sanadiyar wutar lantarki a gidan sa da ke oyemekun, birnin Akuren Jihar Ondo.
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa hadarin ya faru ne da safiyar ranan asabar, 30 ga watan yuli, 2016 yayinda ake shirin tsabtace gida na tazaran wata bayan wata.
An samu rahoton cewa an samu gawarsa ne a saman kwano rike da wayar wuta a sume. Labari ya samu cewan marigayin na kokarin janyo wuta gidansa ta wani fol din makwabta ne. Wata idon shaida ta ce : “Kawai mun waye gari ne muka ganshi a saman kwano rike da wayan wuta. Ina tunanin yana kokarin jawo wuta gidansa ne kawai sai aka dawo da wuta.”
Kakakin ofishin yan sandan Jihar Ondo , Femi JOSEPH, ya tabbatar da hatsarin , yace marigayin na kokarin hada wuta sa ya saba doka.
KU KARANTA : Wasu Samari Sun Tsalleke Rijiya Da Baya
A wata labari mai kama da haka , wata budurwa yar shekara 14 ta rasa ranta a unguwar Alakuko da ke jihar Legas. Yarinyar bakuwa ce ta zo hutu wajen yar uwarta ne, Bukola Oginbajo, bayan ta kamalla karatunta na sakandare . Rahotanni sunce wayan wutan ya fadi kanta ne misalin karfe 10 na safe bayan an dawo da wuta.
The post Ya rasa ransa sanadiyar wutan lantarki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.