Ben Bruce ya baiwa Buhari shawara
Sanata Ben Murray Bruce mai wakiltar Bayelsa ta gabas ya baiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara dangane da kokarin neman hako mai a yankin arewacin kasar nan.
Sanata Ben Murray Bruce
Ben bruce ya bayyana haka ne a shafinsa na twitter, inda ya bayyana ra’ayinsa dangane a kokarin hako mai da aka fara a arewa maso gabas.
“idan da gwamnati zata kashe kudin da take kashewa a kokarinta na nemo arzikin mai a arewa maso gabas wurin harkan noma, toh ina da tabbacin sai sun fi samun kudi a harkan noma”
Ga kadan daga cikin cece kucen da zancen nasa ya janyo.
D-padre yace “aid a ya zamar da kansa ministan noma, amma sai ya zabi ministan mai, yanzu mun san dalili”. Kolapo Abdulkadir yace “Ben Bruce, ya maganan fashe fashen bututun mai da mutanen ka keyi a Neja Delta…..don haka ana hako mai a yankin arewa maso gabas, mun daina dogara da ku”
Shiko Chukwuma Ikonne cewa yayi “anya kuwa akwai mai a arewa maso gabas? Idan ba’a samu ba fa?” Joseph cewa yayi “ Ben Bruce da zaka rinka bata lokaci kana zance mai ma’ana a majalisar dattijai kamar yadda kake yi a twitter, da mun samu canji”. Sai Alebiosu Adeyemi day ace “ina ganin samarin Neja Delta su sake tunani idan har aka samu mai a arewa, saboda zamanin su ya wuce kenan.
A kwana kwanan ne Shugaba Buhari ya umrci hukumar tace mai ta kasa da ta dage da kokarin neman danyen mai a arewa maso gabas. Tun bayan umarnin da Buhari ya bayar, gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa akwai danyen mai da yawa jibge a yankin Bida.
The post Ben Bruce ya baiwa Buhari shawara appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
