Jibrin ya tuhumci Dogara da kokarin yin garkuwa da shi
–Jibrin ya tuhumci Dogara da kokarin garkuwa da shi
–Dan majalisan yace zai amsa kira da jam’iyyar APC ke masa
–Jibrin ya ce yanada kyakkyawan zato jam’iyyar zata goyi bayansa
Dan majalisan wakilai mai wakiltar mazabar Bebeji ta Jihar Kano , Abdulmumini Jibrin ya tuhumci kakakin majalisan wakilai Yakubu Dogara da kokarin yin garkuwa dashi.
Abdulmumin Jibrin
Jibrin ya bayyana hakan ne ta shafin sada zumuntar sa ta twita kamar yadda ya tabbatar da zai amsa kiran da jam’iyyar APC ta masa akan hayagagan da ke faruwa tsakanin sa da kakakin majalisan. Jibrin ya ce bai samu goron gayyatar jam’iyyar ba ta waya ko sako saboda ya daina amsa wayar sa kuma ya daina mayar da sako sabode tsoron kada ayi garkuwa da shi.
“Jam’iyyar ta ce tayi kokarin kirana ta waya ki sako. Ni ban ko wani kira ba, ko na yi , bazan iya zuwa ba saboda yunkurin wasu mutane 4 da dogara da wasunsa suka turo suyi Garkuwa da ni, har sai da lauyoyina suka saman min tsaro daga DSS da ofishin yan sanda. “ Jibrin yace.
“Yanzu zan yi magana akan maganan gayyatar da jam’iyyar APC ta mani da hon jagaba adams. An jawo hankali na akan rahotanni a kafafan yada labarai cewa in gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa ta jam’iyyar mu mai girma. Ja samu wata sako jiya da yamma da ke gayyata ta zuwa hedkwatan jam’iyyar akan hayaniyan da ke faruwa misalin karfe 2 ta rana.”
KU KARANTA : Dogara na cikin tsaka mai wuya: APC ta sammaci Jibrin
Jibrin ya nuna cewa babu wani abin damuwa a cikin wasikar, kuma yanafa yakinin jam’iyyar zata goyi bayansa
“Wasikar bata nuna kwamitin ladabtarwa bane . kuma na amsa cea zan je duk da cewan inada harkokin kai karan kakaki yakubu dogara da wasu 9 hukumomin tsaro da yaki da rashawa. Ina da yakinin jam’iyyar zatayi abinda ya kama ta taimakawa wajen tsarkake majalisan daga rashawa.”
The post Jibrin ya tuhumci Dogara da kokarin yin garkuwa da shi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.