Femi Fani Kayode yayi rubutu game da siyasar Donald Trump
FEMI FANI KAYODE YAYI RUBUTU GAME DA DONALD TRUMP DA KUMA KASAR NAJERIYA.
Jawabin Edita: Tsohon Ministan Najeriya, kuma dan siyasa na PDP, Femi Fani-Kayode ya rubuta wata makala game da dan takarar Shugaban Kasar Amerika, Donald Trump, da kuma siyasar Kasar Najeriya.
Ga tsokaci daga makalar tasa:
Kwanaki nayi wani rubutu mai suna ‘Trump da kuma Musulunci’ inda nake cewa hamshakin Dan kasuwan nan Donald Trump, zai lashe zaben Jam’iyyar sa ta Republican, kana kuma ya lashe zaben Kasar Amerika inda za su kara da Hillary Clinton. Duk da cewa mutane da dama ba za su yarda da ni ba har a Najeriya, amma ban a tababar cewa Trump zai lashe zaben Amerika, kuma ina tare da shi. Mu (Yan Najeriya) abin da muke so, idan an fara muhawara tsakanin yan takarar biyu, Trump ya tambayan mana Hillary Clinton wadannan batu:
Ko shin meyasa Obama bai saka yan Kungiyar Boko Haram cikin yan ta’addan duniya ba har sai karshen shekarar 2014? Bayan an kashe mutanen Najeriya fiye da 100,000. Cikin shekaru 4, da mutanen Kasar Amerika ne, watakila da ya (Obama) fi maida hankali. Da Trump ne shugaban Amerika da yanzu babu wani ISIS, ko wata Kungiya Al-Qaeeda. Da Donald Trump ke mulki, da yanzu ba a yaki a Kasar Syria, da Libya ana zaune lafiya, ba a hallaka Ghaddafi ba. Da ba kashe Jakadan Amerika ba a Bengazi, kai da Yan ‘Brotherhood’ na Egypt basu taba kafa wata gwamnati ba. Da Kasar Afghanistan ta wuce haka. Da ace Trump ne Shugaban Amerika da tuni an lallasa Shababu na Somalia, Israila kuma na zaune kalau, ba a maganar sama ma Iran makami mai linzami. Duk wannan abu sun faru ne lokacin Hillary Clinton tana Sakataren Kasa, dole ta amsa laifin ta daidai da Shugaba Obama.
KU KARANTA: FAFAROMA YACE BA A TABA DAN KWALLO IRIN LIONEL MESSI BA.
A karanta cikakkiyar rubutun Femi Fani-Kayode a shafin san a Turanci
The post Femi Fani Kayode yayi rubutu game da siyasar Donald Trump appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.