Tsohon Shugaban Majalisa, Aminu Tambuwal na goyon bayan Dogara
– Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya kuma Gwamnan Jihar Sakoto, Aminu Tambuwal na bayan Shugaba Yakubu Dogara.
– Haka, Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkar Majalisar Wakilan, A. Kawu Sumaila yana bayan Shugaban Majalisar wakilan, Hon. Yakubu Dogara
Tsohon Shugaban Majalisar wakilan Najeriya kuma Gwamnan Jihar Sokoto na yanzu, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana goyon bayan sa ga Shugaban Majalisar wakilan Kasar, Yakubu Dogara. Ana dai zargin Yakubu Dogara ne badakala a cikin harkar kasafin kudin bana, ana zargin nasa da laifin saka wasu ayyuka da kwangila cikin kasafin wannan shekara. Aminu Tambuwal dai shine wanda ya sauka daga kujerar ta Shugaban majalisar wakilan Kasar, yana daya daga cikin ‘yan Shugaban majalisar Kasar da ba a taba kamawa ko zargin sata ba. Tsohon Shugaban Majalisar, Aminu Tambuwal na kokari shirya yan Majalisar musamman na bangaren Arewa-maso-Yamma da su goyi bayan Shugaban na su Yakubu Dogaran, Jaridar Punch ta rahoto wannan labari. Kowa kuma ya san cewa Dogara mutumin Tambuwal ne tun asali.
READ ALSO: TAKARAN ZABEN SHUGABAN PDP, INA AKA KWANA?
Bayan kokarin shawo kan ‘Yan Majalisun yankin Arewa-Maso-Yammar, Gwamna Tambuwal yana kuma kokari ganin shawo kan ‘Yan Majalisun Kasar Yarbawa, wanda su can ba ruwan su a cikin rikicin, ba su goyon bayan Dogara ko Hon. AbdulMumuni Jibrin. Sai dai kuma ‘yan Majalisun da wuya su manta abin da Tambuwal yayi masu na goyon bayan Dogara a maimakon Femi Gbajabiamila na Kasar Yarbawar, wanda kuma Jam’iyya ta so. Wata Majiyar mu ta bayyana mana cewa, Yan Majalisar ba za su manta da butulcin da Tambuwal yayi masu ba, domin kuwa su suka zabe sa a 2011, da aka dawo shekarar 2015, sai ya nuna masu halin sa.
Haka kuma Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkar Majalisa, Abdurrahman Kawu Sumaila na bayan Yakubu Dogara. Dama dai kwanan Abdulmumin Jibrin ya zargi wasu Gwamnoni da Tsofaffin Yan Majalisu wajen hana sa ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin a ji na sa labarin. Jibrin dai kara zuwa ofihin yan sanda domin binciken zargin da yake, ya kuma yi alkawarin kara tura wasu takardu domin tabbatar da zargin na sa.
The post Tsohon Shugaban Majalisa, Aminu Tambuwal na goyon bayan Dogara appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.