‘Yan bindiga sun afka gidan talabijin NTA a Onitsha
– Yan bindiga kai wa Gidan talabijin din Najeriya NTA da ke Onitsha hari
– Sun banka ma wasu kayayyakin aikin gidan wuta
– Akalla mutane 3 ne aka kama daga cikin wadanda suke da alaka da harin
Ma’aiktatan gidan talabijin na najeriya NTA da ke Onistha ,a jihar Anambra sun ce wasu yan bindiga sun kawo musu hari a rananlaraba 14 ga watan Satumba.
Jaridar Vanguard tace yan bindigan sun banga ma kayayyakin wuta da kuma wasu sassan Star TimesREAD ALSO: Unknown gunmen kidnap pastor in Rivers
Manajan sashen Mr Chris Nwigwe,ya fada ma manema labarai a Onitsha cewa hadarin ya faru ne misalign karfe 1.40 na dare.
“Wasu mutane masu makamai sunyi kokarin cutar da ma’aikatan amma basu samu daman yin hakan ba,sai dai suka banka ma ginin Startimes wuta.”
Wani idon shaida yace an sanya wani bam a dakin mai gadin ,kuma an sanya tayoyi a cikin gidan talabijin domin banka masa wuta.
“An samu musayan wuta tsakanin su da jami’an yan sandan da ke tsaron ofishn. Sun samu banka ma ofishin startimes wuta amma daga baya mutanen da ke kusa sun kashe wuta. Wannan abu bai taba faruwa ba.”
KU KARANTA:Jam’iyyar PDP tana neman Buhari ya sauka daga mulki
Game da cewar jaridar Punch, kwamishanan yan sanda jihar, Mr Sam Okuala, wanda ya je wurin da abin ya faru tare da mayaka bam domin cire bam din, ya tabbatar da cewa an damke mutane 3 a cikin yan barandan.
Ya ce bincike ya fara nuna dalilin kai harin. Okaula ya yabi jami’an yan sandan da karfin halinsu,yace agajin da suka kawo ne ya hana akayi asaran rayuwa da kuma dukiyoyi. Ya gargadi mutane da zantar da hukunci da kansu,kuma ya bada tabbacin cewa sai an gano dalilin hadarin.
“Wadanda ke zantar da hukunci da kansu su shirya fuskantar hukuma, za’a gurfanar da mutane ukun da aka kama a kotu idan aka gama gudanar da bincike.” An sanya motocin fatrol 3 a gaban gidan domin tabbatar da tsaro.”
The post ‘Yan bindiga sun afka gidan talabijin NTA a Onitsha appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.