Ya kamataBuhari ya tuntubi masana tattalin arziki iri na -Sanusi
– Sarki Muhammad Sanusi II na kano ya baiwa gwamnatin shugaba buhari cewa ta nemi shawaran kwararrun masana tattalin arziki domin magance durkushewar tattalin arzikin kasa
– Sanusi lokaci yayi da za’a nemi mafita daga cikin matsalan tattalin arzikin da ake ciki.
Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya baiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ya nemi shawaran manyan kwararrun masana tattalin arziki ciki da wajen gwamnati domin samun mafita daga matsalar tattalin arzikin kasa.
President Muhammadu Buhari
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, yayi magana a ranan laraba,14 ga watan satumba a hawan nasarawa a gidan gwamnatin jihar Kano.
Jaridar Daily Post yace yanzu ne lokacin da duk masu zurfin tunani zai nemi mafita daga cikin durkushewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.
Yace yawancin manyan mutane na yaudarar kansu ne saboda da bashi suke rayuwa.
KU KARANTA:Shure-shure Boko Haram take yi-Inji Sojojin Najeriya
Kana Sanusi yayi kira da masu hannu da shuni cewa su taimaki maras hali a unguwa saboda gusar da wahaln da suke ciki. Ya kara da cewa duk da bambancin addini da harshe, mu cigaba da taimaka wa kasa da addua ga cigaban kasan nan.
A bangare guda, Muhammadu Buhari ya mika sakon sallan sa cewa jam’iyyar PDP sunyi kaca-kaca kasa shekara 16 mulkin su.
Yace: “Ina son yan najeriya su sani cewa abunda wannan gwamnati ta mallaka bayan shekaru 16 mulikin PDP shine rashin ajiya, ba aiki, ba titunan jirgin kasa, ba hanyar mota, babu tsaro.”
The post Ya kamataBuhari ya tuntubi masana tattalin arziki iri na -Sanusi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.