An hallaka ‘yan Boko haram a wata shara
–Rundunar sojin Najeriya sunyi wata shara wanda yayi sanadiyar mutuwan wasu yan kungiyar Boko Haram
–Rundunar Sojin sun kwato wasu makamai
– Sojin sunyi alkawarin cigaba da tabbatar da zaman lafiya
A cigaba da yunkurin kawar da yan kungiyan Boko Haram a kasar, wata rundunar sojin najeriya sunyi musayan wuta da wasu yan kunyigan boko haram a wasu sassan jihar Yobe.
A wata jawabin da kakakin hukumar soji , Kanal Sani Usman Kukasheka, ya bayyana cewa rundunar sojin Operation Lafiya Dole sun yi wata shara a ranan laraba 14 ga watan satumba. An kwato makamai a hannunsu.
Karanta jawabin da yayi:
“Bisa ga rahoton da muka samu na ayyukan ragowan yan boko haram a unguwar Jororo da Tombaeji a karamar hukumar Geidam a jihar yobe, rundunar sojin Operation Lafiya Dole sun kai wata shara da safiyar ranan laraba, 14 ga watan Satumba.”
KU KARANTA:Shure-shure Boko Haram take yi-Inji Sojojin Najeriya
“Rundunar sojin sunci karo da yan boko haram a wurin Gajire inda sukayi musayan wuta wanda aka kwashe minutuna 15 ana yi.”
“Rundunar sojin sun kashe guda 4 daga cikinsu kuma sun kama guda daya. Sun kwato General Purpose Machine Guns (GMPG), 2 AK-47 Rifles and 144 rounds of 7.62mm da babur guda 2 daga hannun yan boko haram din.”
“Rundunar sojin sun cigaba da fatrol a unguwan la’alla akwai suran ragowan su wadanda ke boye a wurin. Mazajen Operation lafiya dole sun cigaba a ayyukansu na kawar da ayyukan yan boko haram a wurare dabn-daban.”
The post An hallaka ‘yan Boko haram a wata shara appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.