An haifi wani yaro a tsakiyar teku cikin jirgin ceto
Ana haihuwa a wurare iri-iri, amma wannan jaririn na musamman ne, an haife a tsakiyar teku a cikin jirgin ceto.
Iyayen jaririn Faith da Otis suna kokarin guduwa daga kasar su, su tafi nahiyar fararen fata ta hanyar ruwan da suka hada kasashen dan zama yan gudun hijira, Faith hakika tana bukatar samun kubuta saboda tana da tsohon ciki ga yara guda 2.
Suna tsakiyar tekun a cikin wata jirgin ruwa da wasu mutane kimanin 200 yan gudun hijira, lokacin da matar ta fara jin ba dai-dai ba, ga nakuda ta taso, dan haka taga bata da wani zabi sai dai ta haihu a gurin da ba mai ceto kuma basu tsammanin wani ze iya kawo dauki.
Allah maji roko, sai gashi ya aiko mana da agaji lokacin da muke da tsananin bukatar shi, kullum ubangiji yana da tanadi ga bayinsa da suka yi imani da shi, wata babbar jirgi MS Aquarius yazo ya kawo mana dauki.
Jirgin na wasu yan kasar Germany ne wanda yake aiki tsakanin tekun dan taimakon jama’a, ita kungiyar manufarta ba wani dan Adam da ya cancanci ya nutse a ruwa, dan haka jirgin da ya gan su. Sai ya ceto duka mutanen, a ranar jirgin ya ceci mutum 300 kuma wannan ya zama abin al’ajabi ga iyayen jaririn.
Mutanen da ke cikin jirgin sun yi farin ciki da alfaharin ganin sun taimaka gurin haihuwar yaron, basu taba tsammanin kubuta daga tashin hankali da mutuwa a kasar su ba, sai gashi Allah ya kawo mutanen kirki da suka taimake su.
The post An haifi wani yaro a tsakiyar teku cikin jirgin ceto appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.