Conte ya bayyana yadda Chelsea zata fuskanci Liverpool
– Antonio Conte yace John Terry ya samu rauni dan haka ba ze samu doka wasar Liverpool ba
– Conte yana tsammanin yan wasan gaba na Liverpool zasu kawo ma Chelsea matsala
– Dan kasar Italy ya tabbatar da cewa David Luiz ze doka wasa a mai makon John Terry.
Mai horarwar Chelsea Antonio Conte ya bada haske kan yan wasan da zasu fara doka wasa ranar Juma’a da zasu gabza da kungiyar Liverpool.
Lokacin da yake magana da manema labarai dan gane da wasar, Conte yace mai tsaron baya David Luiz ze doka wasa a mai makon kaftin John Terry da ya samu rauni.
Antonio Conte da John Terry
Luiz ze yi wasar shi ta farko tun bayan dawowarshi kungiyar Chelsea daga kungiyar PSG a rana ta karshe ta rufe kasuwar cinikayyar yan wasa bayan kaftin John Terry ya samu rauni a kafa.
“Muna tsammanin zeyi wasa da kyau” Conte ya fada ma mane ma labarai” mun San David dan wasa ne mai kyau.
Conte yayi magana akan wasar da yake tsammanin Liverpool zasu doka.
“Liverpool kungiya ce mai kyau, suna doka wasa da kyau, kuma sun saya yan wasa kwararru. Yace”Klopp mai horarwa ne mai kyau, yana cikin manyan masu horarwa na duniya.
Jurgen Klopp
Chelsea ta fara wasa a kakar bana da kyau, suna matsayi na 2 a jadawalin premier league, inda suka yi wasa 4, suka yi nasara sau 3 da kunnen doki 1.
Liverpool. Kuma suna matsayi na6, sun yi nasara sau 2 da kunnen doki 1, an cisu sau 1.
The post Conte ya bayyana yadda Chelsea zata fuskanci Liverpool appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.