Abubuwa 4 da ake harsashen Jonathan ya tattauna da Babangida
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Minna a jihar Niger ranar Talata 13 ga Satumba inda ya tattauna da tsaffin shuwagabannin kasa janar mai murabus Ibrahim Babangida da janar mai murabus Abdulsalami Abubakar a lokutta daban.
Ba’a bar masu daukar labarai halartar tarurrukan ba, ba’a kuma bada jawaban bayan tarurrukan ba, amma Jonathan ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa zai ci gaba da hada zumunci cikin kasa.
Ga harsashen da the Punch tayi na abubuwan da shugabannin biyu suka tattauna
1.Yakin da Buhari keyi kan cin hanci da rashawa
Wadansu na cewa taron bai rasa nasaba da yakin shugaba Buhari kan cin hanci da rashawa da kuma yadda yakin yake shafar ‘yan uwan Jonathan da kuma matarsa Patience.
2.Zaben jihar Edo
A wani abinda ba’a zata ba, hukumar zabe (INEC) ta daga zaben gwamnan jihar Edo da sati biyu, abinda yasa jam’iyyar Peoples Democratic Party tayi zargin cewa shugaba Buhari yayi haka domin samarma jam’iyyarsa lokaci. Ana zaton taron tsakanin GEJ da IBB ya tattauna batun zaben da aka daga, zaben 2019 da kuma halin da jam’iyyar hamayyar take ciki.
KU KARANTA: NAIJ.com ta zamto gwarzon jaridar yanar gizo a Najeriya
3.Tsagerun Neja Delta
A tarukkan da Babangida da Abubakar sukayi da tsohon shugaba, sun nuna damuwarsu kan karuwar hare-haren tsagerun Neja Delta.
4, Lafiyar Babangida
Babangida ya bayyana rashin lafiyarsa cikin watannin da suka wuce, inda yake karyata cewa yana kwance baya iya tashi, koko ya Sami shanyewar jiki. Babangida ya fadi haka a wata liyafar ban girma da aka shiryawa mai shari’a Fati Lami Abubakar, tsofuwar babbar alkalin jihar Niger inda daga karshen bikin saida aka taimaka masa ya mike.
The post Abubuwa 4 da ake harsashen Jonathan ya tattauna da Babangida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.