Abinda yasa Oshiomole ya firgita – Nyesom Wike
Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya mayar da martani dangane da zargin da gwamnan jihae Edo Adams Oshiomole yayi na cewa shi Wike, shi ke daukan nauyin dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin jam’iyyar PDP, ta hanyar kashe makudan kudaden da suka kai naira biliyan 2 da daukan hayan tsageru don su hana kowa sakat ranar zaben.
A lokacin da yake jawabi yayin ganawarsa da hadakan jam’iyyun kasar nan (IPAC) a fadar gwamnatinsa dake Fatakwal, Wike ya shawarci gwamnan Edo da kada ya zarge shi game da sakamakon zaben, sa’annan ya daina yayata karairayi akan sa.
Gwamna Wike yace wanda Oshiomole ya taba tare ne yana fada min, kyale mutanen nan, basu san abin da muke tattaunawa ba. Toh idan Oshiomole ya karaya da zaben ne, toh kada yaga laifina. Ya iya kawo shugaban kasa jihar tare da gwamnoni 10, amma hakan bai ishe shi ba. Sai kawai don gwamnonin PDP 2 sun ziyarci jihar, sai Oshiomole ya fara fargaba? Ya kamata, Oshiomole a shekarunsa ya daina karya.
KU KARANTA:Gwamna Wike Ya Kori Kwamitin Ciyamomin
Me yayansa zasu ce idan suka ganshi a a haka, idan ba zaka iya cin zabe ba, ba zaka iya ci ba, koda sau nawa zaka rubuta rahoton tsaro. Ban san yaushe Oshiomale zai daina karya ba. Me yasa yake tunanin zai cigaba da yaudarar mutane ne? wannan shi ne Oshiomolen daya yabawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan tsarin zaben gaskiya daya kawo. Da haka ne Oshiomole yaci zabe a karo na biyu.
Sai gashi a yau, duk inda Oshiomole yace yana cin mutuncin tsohon shugaban kasa, idan yau shugaban kasa Buahri ya sauka daga mulki, haka Oshiomoe zai yi mai.
A wani labarin kuma, daruruwan yan jam’iyyar APC da na UPP ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a jihar Edo, hakan ya faru ne alhalin saura sati biyu a gudanar da zaben gwamnan jihar, ranar 28 ga watan Satumba.
The post Abinda yasa Oshiomole ya firgita – Nyesom Wike appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.