Hira: Ka raina ma Buhari kasha wahala – Ojudu
A wata hira da Sanata Femi Ojudu, mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkokin siyasa yayi da Michael Abimboye na NAIJ.com yayi magana kan matakan siyasa da shugaban ke dauka, zabukan 2019 da kuma shawo kan rigingimun dake cikin APC.
Menene aikinka a matsayin mai bada shawara kan harkokin siyasa?
Abu ne a bayyane, Ina tattara bayanan sirri na siyasa, in nazarcesu, in kuma bada shawara yadda ya kamata
Yaya kwarewarka a matsayin tsohon dan jarida ya shafi aikinka na mai bada shawara a harkokin siyasa?
Senator Babafemi Ojudu
Nayi rohotanni game da gwamnati da kuma mulki na tsawon shekaru 28. Inada babban digiri na masters kan kimiyyar siyasa. Da ni dan gwagwarmaya ne kuma dan siyasa. Na tsaya takarar zabe kuma naci, saboda haka inada masaniya game da mulki a Najeriya da sauran wurare. Na karade kasar nan da kuma wasu wurare a duniya. Na Karanci tarihin manyan mutane a duniya dama wadanda ba manyan ba wadanda suka rubuta da kansu koko aka rubuta game dasu. Nasha wahalhalu kan matsayi na. Zani iya takama cewa rayuwata da aikina sun shirya ni domin wannan aikin.
Ba’a san shugaban da siyasa ba, yaya kake taimakon shugaban a matsayinsa na shugaba da kuma kyamarsa kan siyasa?
Zanyi kuskure idan nace mutunen da sau biyu yana shugabancin kasar nan ba’a sanshi da siyasa ba. Ka raina ma Buhari kasha mamaki.
Ana batun matsatsi a kasar yanzu, kana da wannan ra’ayin, kuma me shugaba keyi game da haka?
KU KARANTA:Wasika: Don Allah Shugaba Buhari, ka biya malamanmu albashinsu
Nima ina jin matsin, haka kuma shugaban kasar, da mataimakinsa da kuma duk wanda e cikin gwamnatinsa. Muna aiki tukuru domin shawo kan matsalolin,kuma ba da wasa ba, a’a matakai masu dorewa muke son dauka
A matsayinka na mai bada shawara kan siyasa, kana iya bada shawara yadda za’a bar shariar shugaban majalisar dattawa a siyasance?
Kayi maganar shari’a, alkalai ke yin shari’a. Kuma alkalai nada nasu ‘yancin kamar bangaren zartaswa. Saboda haka zai yi wuya in tsoma bakina cikin ayyukan alkalai
The post Hira: Ka raina ma Buhari kasha wahala – Ojudu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.