Gasar iya ado: Patience Jonathan ko Diezani Alison-Madueke
Ba cuku-cukun gwamnati kadai ke akwai cikin siyasa ba, akwai saura kamar iya sa kaya da kuma kwalliya. Dauki wadannan matan guda biyu, ga manyan kudi cikin daloli, ga kuma iya shiga.
Dame Patience Jonathan, uwargidan tsohon shugaban kasan Najeriya da kuma wata ‘yar siyasa Mrs Diezani Alison-Madueke, kuma mace ta farko da ta rike mukamin shugaban OPEC. Wadannan mata akwaisu da dogon buri, kyawu da kuma iya kwalliya.
An haifi Mrs Diezani K. Alison-Madueke a shekara ta 1960 watanni kadan bayan Najeriya ta samu ‘yancin kanta, tana auren tsohon shugaban dakarun ruwan Najeriya, Alison Madueke, kuma ta kasance mace ta farko da ta rike mukamin ministan sufuri cikin Yuli, 2007.
An haifi Patience Faka Jonathan a shekara ta 1957. Uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Ta kuma rike mukamin babban sakatare a gwamnatin jiharta ta Bayelsa. Wadannan matan na daukar hankalin jama’a wajen iya Shigarsu. Bari mu gani wa zata fi wata cikin wannan gasar.
Iya tsayuwa a tsanake
Diezani Alison-Madueke ta rike manyan mukamai ukku na gwamnatin tarayya. An nadata ministan sufuri cikin Yuli 2007. Ranar 23 ga Disamba aka maida ta ministan ma’adinai da karafa
Tsayuwar gefe
An haifeta garin Port Harcourt, kuma ta samu takardar kammala sakandare a 1976, yayin da taci jarrabawar Afrika ta yamma (WASSCE) a 1980.
KU KARANTA:Muna neman Ibrahim Shema ruwa a jallo – EFCC
Launin shuni na mata kyau
Bayan mataimakin shugaban kasa Gooodluck Jonathan ya zama shugaban kasa mai rikon gado, a Febrairu 2010, ya sake sabbin ministoci ranar 6 ga Aprilu 2010 inda yaba Alison-Madueke ministan albarkatun mai
Na fika kyawu
A shekara ta 1980 ta samu takardar shedar kammala karatun malanta (NCE) kan lissafi da hallitu daga makarantar koyon kimiyya ta jihar Rivers da ke Port Harcourt, daga nan ta wuce zuwa jami’ar Port Harcourt inda ta karanci hallitu da halayen dan Adam to wa zaka ce yafi iya ado?
The post Gasar iya ado: Patience Jonathan ko Diezani Alison-Madueke appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.