Babu wanda ya isa ya taba Patience Jonathan
– Sanatocin Jam’iyyar PDP sun sha alwashi kare Tsohuwar Uwargidan Najeriya, Patience Jonathan daga tuhumar Hukumar EFCC
– Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa na binciken yadda Mrs. Patience Jonathan da samu wasu kudi har dala miliyan 19.8 a akaun
– Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka Madam Patience tana Abuja domin ganin yadda za ta fita lafiya daga hannun EFCC
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya tana binciken yadda Tsohuwar Uwargidan Najeriya Mrs. Patience Jonathan da samu wasu makudan kudi har dala miliyan 19.8 a akaun din ta. Sai dai ‘Yan majalisun dattawa na Jam’iyyar PDP sun shirya fada da Hukumar saboda garkame mata akaun da aka yi. Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka Madam Patience, matar tsohon Shugaba Jonathan tana Birnin Abuja domin ganin yadda za ta fita lafiya daga hannun EFCC.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Sanatocin PDP sun fara ganawa tuna Ranar Alhamis domin ganin sun taka birki ga Hukumar EFCC wajen binciken Matar tsohon Shugaban Kasar da take yi. Wata majiyar ta nuna cewa Sanatocin sun dukufa da zama a kai, a kai domin ganin yadda za suyi maganin Hukumar EFCC. Sanatocin adawar Kasar dai sun tabbatar da cikakkiyar goyon bayan su ga Tsohuwar Uwargidan Patience Jonathan.
KU KARANTA: EFCC za tayi ram da Patience Jonathan-Magu
Wani dai da bai bayyana sunan sa ba, yake cewa idan lokacin yayi, za su bayyana Sanatocin da ke da hannu cikin wannan aiki. Yake cewa dole su hada kai, don ba su da gaskiya ko kadan. EFCC dai tana binciken wasu kamfanin da aka samu da kudi har dala miliyan $15,591,700. Sai dai tuni Patience Jonathan tayi ikirarin cewa kudin nata ne.
Tuni dai Hukumar ta rufe wadannan akaun, sai dai Lauyan Tsohuwar Uwargidar yace akaun din na Madam Patience ne da kuma na mahaifiyar ta.
The post Babu wanda ya isa ya taba Patience Jonathan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.