Anyi jana’izar Mahaifin Tompolo
An binne Mahaifin Tompolo
Mutane kimanin ne suka rasa rayukan su yayin zuwa wajen jana’izar Cif Thomas Ekpemupolo, Mahaifin gawurtaccen tsageran nan da Gwamnatin Tarayya take nema ido rufe watau Government Tompolo. Hukumar dillacin Najeriya ta Kasa NAN, ta bayyana cewa wasu mata da namiji guda sun nutse a hanyar su ta zuwa Jana’izar mahaifin Tompolo. Mutanen dai sun fito ne daga Yankin Kurutie da Ogulaha na Kasar Gbaramatu.
Ta dai ritsa da wasu yayin da suke kokarin zuwa birne gawar wani, mutanen dai sun hau wani jirgin ruwa ne mara lafiya a Garin Warri domin halartar jana’izar Marigayi Cif Thomas Ekpemupolo, wanda shine Uban Tsageran nan da ake nema ruwa a jallo-Tompolo. An fara bikin Jana’izar Cif Ekpemupolo ne a ranar Jumu’a nan. Wani Shugaba Lawani a Yankin ya bayyana cewa yayin da suke kokarin jana’izar Marigayi Cif Thomas Ekpemupolo, sai kwatsam suka samu labarin cewa ruwa ya kuma ci wasu yayin da suke kokarin hallartar wannan jana’izar.
Da fari dai an bayyana cewa mutane biyu kacal ne suka rasu, sai daga baya labari ya zo cewa mutanen da suka rasun har sun kai hudu. Namijin da ya rasu dai, shi mutumin Arewa ne, kuma kasuwanci ya kawo sa, ya zo saida kaya ne kurum wajen jana’izar, ashe da rabon ba zai yi rai ba.
KU KARANTA: Tsagerun Avengers sun gargadi Muhammadu Buhari
Wani Jami’in ‘Yan Sanda na Yankin mai suna SP Celestia Kalu, ya dai tabbatar da faruwar wannan abin takaici. SP Celestia Kalu wanda shine ke magana da yawun bakin ‘Yan Sandan Jihar Delta yake cewa : ‘Ina sanar maku da aukuwar wannan mummunar abu a Jihar nan. Wani jirgin ruwa na Yamaha kirar AW-9 ya samu hadari a cikin Rafin Warri…Bayan da Injin jirgin ya samu matsala, sai ya nutse cikin ruwa.’
Mai magana da yawun bakin ‘Yan Sandan Jihar SP Celestia Kalu ya bayyana cewa yanzu haka ana ta kokarin ceto ran wanda suka rasu.
The post Anyi jana’izar Mahaifin Tompolo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.