Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan tafiyar shi taron UN
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso gida Najeriya da sanyin safiyar nan daga tafiyar shi da yayi zuwa kasar Amurka inda ya halarci taron kasashen duniya na 71 (UNGA 71) a New York 25, ga watan Satumba 2016.
Shugaba Buhari ya iso Najeriya bayan taron da ya halatta na kasashen duniya na 71.
Shugaban kasar cikin jawabin sa bayan taron yace” hakika tafiyar shi ta samu dimbin nasarori kuma ya rattaba hannu na yarjejeniyar tabbatar da canji.
Lokacin da yake bayyana ma manema labarai abun da aka tattauna a New York, shugaban ya faffadi manya-manyan abubuwan da aka tattauna a lokacin taron kuma yayin karin haske wanda ya zama sako karara ga shugabanni kasashe na duniya.
Shugaba Buhari yana gaisawa da shugaban hafsan sojojin sama.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana gaisawa da sugaban ma’aikata Alhaji Abba kyari.
Shugaba Buhari yana gaisawa da gwamnan Lagos Ambode Akinwunmi.
The post Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan tafiyar shi taron UN appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
