An kama wani mai anfani da kafar sadarwar zamani a Jihar Katsina
A wani labarin da aka buga a shafin majiyarmu ta Premiums Times na nuni da cewa an kama mai jaridar yanar gizon nan ta Cliqq Magazine dan asalin jihar Katsina wato Jamil Mabai a ranar Litinin din da ta gabata a garin Kaduna sakamakon yada wani labari a kan gwamnatin Aminu Bello Masari na jihar Katsinar.
Majiyar ta rawaito mana cewa tuni kotun jihar Katsina ta ingiza keyarsa zuwa gidan maza sakamakon tuhumarsa da wasu laifukan da suka shafi cin zarafi.
Sai dai majiyar tamu ta tuntubi Abdu Labaran mai ba gwamna shawara a kan harkar labarai, amma ya ce ba ruwan gwamnati ga maganar.
Haka kuma a wani labarin an nuna ana zargin an kama Mabai ne sakamakon ya wallafa wani labari na cewa gwamnan jihar ya sawo Makaru na silba har guda 3000 a kan naira dubu 40,000 a kowace da za a raba a masallatan jihar.
Za a ci gaba da sauraron shari’arsa a ranar Litinin mai zuwa, a inda ake tunanin watakil a ranar a sami amsar belinsa.
Shin ya kuke kallon wannan kamun da aka yi wa Jamil Mabai, an yi sa bisa ka’ida ko an waske wadokar ‘yan fadin ra’ayi.
The post An kama wani mai anfani da kafar sadarwar zamani a Jihar Katsina appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
